DA DUMI-DUMI: Tinubu, Sanwo-Olu da Ganduje sun isa Ibadan, Don ganawa da Deliget Din Jihar Oyo

0

DA DUMI-DUMI: Tinubu, Sanwo-Olu da Ganduje sun isa Ibadan, Don ganawa da Deliget Din Jihar Oyo - Dimokuradiyya

Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, da gwamna mai ci, Babajide Sanwo-Olu da takwaramsa na jihar Kano, Abdullahi Ganduje sun isa Ibadan babban birnin jihar Oyo, a wani bangare na yakin neman zabe.

An ce Tinubu da magoya bayansa sun je Ibadan ne domin jan hankalin wakilan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa da za a yi a ranar 6 ga watan Yuni na wannan shekara.

Wadanda ke cikin ayarin Tinubu sun hada da tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kasim Setthima, Sanata Tokunbo Abiru, Bosun Oladele, Rotimi Makinde, Sanata Rilwan Soji Akanbi, Sanata Dayo Adeyeye, Bosun Oladele da Wasiu Eshinlokun.


Download Mp3

A filin saukar jiragen sama na Ibadan domin tarbar dan takarar shugaban kasa akwai ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Sanata Teslim Folarin, Akeem Adeyemi, Akin Alabi, tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, Dokun Odebunmi, Sanata Fatai Buhari, Idris Adeoye da shugaban jam’iyyar APC a jihar, Isacc Omodewu. .

Sauran sun hada da Dapo Adesina, Sunday Adepoju, da Ibrahim Olaifa.

A lokacin gabatar da wannan rahoto, Tinubu na ganawa da wakilan ne a wata cibiyar taron da ke Ibadan

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy