Da Dumi-dumi: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Dan Takarar Sanata Na Jam’iyyar APC A Kano
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC A.A Zaura.
An yi garkuwa da mahaifiyar dan siyasar, Hajiya Laure Mai-Kunu da sanyin safiyar Litinin (yau) gabanin kiran Sallar asuba.
Shugaban karamar hukumar Ungogo, Engr. Abdullahi Garba Ramat, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami’an tsaro sun sanar da shi faruwar lamarin a hukumance.
Ya ce an yi garkuwa da Hajiya Laure ne a gidanta da ke mazabar Rangaza a karamar hukumar ta ungogo.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na safiyar ranar Litinin (yau) inda ya kara da cewa tuni rundunar ta tattara jami’anta da nufin ceto wanda lamarin ya shafa tare da cafke wadanda ake zargin.
KARANTA WANNAN LABARIN
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya amince da kaddamar da wani kwamiti kan batun sauya sheka.
Kwamitin dai na da alhakin tuntubar duk masu son tsayawa takara da kuma ‘yan jam’iyyar da suka koka kan sakamakon zaben fidda gwani da aka kammala.
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da aka ga wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da PDP a wani taro da shugaban NNPP na Jigawa, Malam Aminu Ibrahim Ringim ya shirya a gidansa na kashin kansa da ke Kano.
Daga cikin manyan ‘yan siyasar akwai ‘yan takarar gwamna uku: Sanata Sabo Muhammad Nakudu, tsohon mataimakin gwamna, Ahmad Muhammad da Bashir Adamu Jumbo.
Sauran sun hada da tsohon dan majalisar wakilai, Honarabul Gausu Boyi Ringim, dan majalisar jiha, Hon.Sule Musa Dutse, tsohon shugaban Dutse, Bala Yakubu Yargaba, da sauran manyan magoya bayan PDP da APC.
Kwamitin sulhu, wanda ke karkashin jagorancin Sanata Bello Maitama, shi ne don hana sauya sheka daga ‘ya’yan da suka koka da su gabanin zaben 2023.
