Dalilan da suka sanya ban halarci Zaɓen Fidda Gwani na Shugaban Ƙasa — Nwajiuba

0

Dalilan da suka sanya ban halarci Zaɓen Fidda Gwani na Shugaban Ƙasa — Nwajiuba - Dimokuradiyya

Dalilan da suka sanya ban halarci Zaɓen Fidda Gwani na Shugaban Ƙasa — Nwajiuba

Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana cewa rashin Zuwan sa a zaɓen fitar da Gwani, ya faru saboda ƙin tura Tikitin Takarar ga yankin Kudu maso Gabas.

Nwajiuba wanda ya kasance tsohon Ƙaramin Ministan Ilmi ya kasance bai halarci taron a lokacin da shi da sauran ƴan takara aka kira su domin yin jawabi a daren Talata, kafin fara zaɓen Fidda Gwani na Shugaban a Eagles Square.

A cikin sanarwar daya fitar a ranar Laraba, Chinedum Nwajiuba tsohon Ministan, wanda ya taso daga yankin Kudu, yace fahimtar sa na shiga siyasa don yana so ne ya kawo cigaba.

Yace “da wannan fahimtar, ya kamata ace Tikitin Takarar yazo daga yankin Kudu, musamman Kudu maso Gabas.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy