Dan Gwamna Nasir El-rufa’i Ya Sha Wani Alwashi, Idan Peter Obi Ya Zama Shugaban kasa

0

Dan Gwamna Nasir El-rufa’i Ya Sha Wani Alwashi, Idan Peter Obi Ya Zama Shugaban kasa - Dimokuradiyya

Bashir El-Rufai, dan Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya yi alkawarin aiwatar da wasu abubuwa, idan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya lashe zaben 2023 mai zuwa.

Bashir ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau cewa zai haura Aso Rock da ke Abuja da kuma Dutsen Zuma Rock a Jihar Neja.


Download Mp3

Baya ga haka zai kuma rubuta Ɓaro-Ɓaro jikin dutsen guda biyu cewa a “Bashir El-Rufai Dan akuya ne”.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a baya, Bashir ya yi ikirarin cewa yana sane da wadanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ware a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Duk da cewa bayan wannan magana ta sa ya kasa bayyana sunayensu saboda wasu bayanan sirri ne.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy