Darakta Aminu Saira Ya Fadi Ranar Da Zasu Dawo Nuna Shirin Labarina
Game da wannan shiri mai dogon zango wato labarina da mutane da dama suke ta jiran dawowar su yau shararren darakta aminu saira yayi magana akan ranar da zasu dawo.
Daraktan yanwalla a shafin sa na Instagram tare da daura wassu hotunan da suka dauka a wajen daukar shirin sai yayi sanarwa kamar haka.
“SANARWA! SANARWA!
ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAH Muna Sanar da Ma’abota Kallon Wannan Shiri na #LABARINA series cewa In sha Allah Zamu cigaba da daukar Season 5&6 . Muna kuma Sa ran Fara Haska muku shi a wata mai kamawa (JULY 2022) in sha Allah. Muna baku hakurin akan dogon Jira da kukai, muna Godiya ga kyaunar ku Gare mu Allah yabar Zumunci @sairamoviestv #LABARINA 5&6″
