Ecuador vs Nigeria: Super Eagles ta rasa wasan ta a hannun Peseiro karo na biyu

0

Ecuador vs Nigeria: Super Eagles ta rasa wasan ta a hannun Peseiro karo na biyu - Dimokuradiyya

Ecuador vs Nigeria: Super Eagles ta rasa wasan ta a hannun Peseiro karo na biyu

Ƙungiyar Wasan Ƙwallon Ƙafa ta Super Eagles ta kammala wasan ta da rashin nasara a hannun Ecuador a filin wasa mai cin mutane 25,000 Red Bull Arena dake garin Harrison, New Jersey.

An taka ledar da sanyin safiyar ranar Juma’a, inda Najeriya ta rasa wasan ta da ci 1-0 ga Ecuador, a Sabon mai horasa da ƴan wasa José Santos Peseiro.


Download Mp3

Ƙwallon da ɗan wasa Pervis Eztupiñán ya sharara, ita ce ta baiwa ƙasar Ecuador nasara a Wasan, baya ga ɗaukar mintuna 70 sannan wannan nasara ta samu.

A wasan farko da sabon Kocin ya fita da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa, Najeriya ta rasa wasan da ci 2-1 a hannun Mexico wanda ya gudana a Halves ta Dallas ranar Asabar.

Wasan tsakanin Ƙungiyar da Ƙasar Ecuador ya zo ne sati guda bayan Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Super Eagles ta Samu nasara akan Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Leone Stars ta Ƙasar Sierra Leone a filin wasa na MKO Abiola, Abuja a wasan samun nasarar cin kofin Nahiyar Afirka na Shekarar 2023.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy