EFCC Ta Kama Ƴan Damfara Ta Intanet 92 A Jihar Rivers

0

EFCC Ta Kama Ƴan Damfara Ta Intanet 92 A Jihar Rivers - Dimokuradiyya

Jami’an Hukumar Yaki da masu yiwa Tattalin Arzikin kasa Ta’annati EFCC shiyyar Fatakwal sun kama wasu mutane 92 da ake zargi da damfarar yanar gizo (wato Yahoo Boys).

Hukumar ta EFCC tayi nasarar kama bata garin ne a wani samame da suka kai a wurare daban-daban a garin Fatakwal dake jihar Ribas.

A wata sanarwa da hukumar ta EFCC ta fitar a yau Juma’, ta hannun shugaban sashin yada labarai da hulda jama’a, Wilson Uwujaren, ya ce an kama wadanda ake zargin ne da laifin zamba ta yanar gizo a Choba da Ada George dake a Fatakwal.


Download Mp3

Ya kara da cewa biyo bayan rahoton sirri da suka samu ne, ya sa suka shirya sumamar wuraren.

Sanarwar ta ce binciken da aka yi na na’urorin da aka gano daga hannun wadanda ake zargin sun nuna cewa 64 daga cikinsu na da abubuwan da ba su dace ba a cikin wayoyinsu da sakwannin imel.

Hukumar ta ce za a gurfanar da wadanda ake tuhuma a gaban kuliya bayan bincike ya kammala akan su.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy