Fadar Shugaban Ƙasa Ta Magantu Kan Kalaman Tinubu Ga Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Magantu Kan Kalaman Tinubu Ga Shugaban Kasa - Dimokuradiyya

Fadar shugaban kasa ta mayar wa da Bola Ahmad Tinubu martani kan kalaman sa na cewa in ba dan shi ba da Buhari bai Kai labari a zaben da ya gabata ba.

A cewar fadar babu wanda ya isa ya ce shi kaɗai ya yi uwa ya yi makarɓiya har Shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan karagar mulki a zaɓen 2015.

Mai magana da yawun shugaban Garba Shehu ne ya fitar da sanarwa inda ya ce abin da ya wuce a baya bai kamata ya zama abin da za a yi la’akari da shi ba a wurin zaɓen da ke tafe.


Download Mp3

Ya bayyana cewa abin da ke da muhimmanci a yanzu shi ne a zaɓi shugaba da zai kawo ci gaba a Najeriya.

Ya bayyana cewa akwai waɗanda suka ba shugaban shawara da ya ƙara takara da waɗanda suka gina jam’iyya inda ya ce babu wani mutum guda da zai iya cewa shi ya yi duka waɗannan shi kaɗai.

Sai dai ana ganin wannan sanarwar da Fadar Shugaban Najeriyar ta fitar ba ta rasa nasaba da wasu kalamai da Bola Ahmed Tinubu ya yi masu kama da gori inda ya ce shi ya taimaka Buhari ya ci zaɓe.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy