Fayose ya taya Atiku murnar lashe Zaɓe, ya yabawa haƙurin Wike

0

Fayose ya taya Atiku murnar lashe Zaɓe, ya yabawa haƙurin Wike - Dimokuradiyya

Fayose ya taya Atiku murnar lashe Zaɓe, ya yabawa haƙurin Wike

Tsohon Gwamnan Jahar Ekiti Ayodele Fayose ya taya Atiku Abubakar murna daya samu nasarar lashe Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar PDP daya wakana a satin daya gabata a Abuja.

Fayose ya dai yi shiru tun bayan zaɓen Fidda Gwani na Shugaban Ƙasa. Inda ya yabawa Gwamna Nyesom Wike wanda yazo na biyu.

Fayose, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar PDP, na ɗaya daga cikin wanda suka kasa samun koda ƙuri’a ɗaya ba.

Atiku, ya zama Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a PDP na Babban Zaɓen Shekarar 2023, bayan ya samu Ƙuri’a 371 akan Wike wanda ya samu ƙuri’a 237.

“A saboda haka ina taya murna ga Alhaji Atiku Abubakar akan samun nasarar da yayi na zama Ɗan Takarar PDP. Ina kuma yabawa Gwamna Nyesom Wike daya zamanto mai haƙuri, da Jajircewa”, inji rubutun da yayi.

Yace yanayin yanda ake siyasa a ciki da wajen PDP zai kasance a zuciyar ƴan Najeriya

Ya bayyana cewa yafi dacewa mutum ya hango nasarar Jam’iyyar, bawai yayi shiru don ya faɗi a zaɓen fidda Gwani ba.

Atiku dai tuni ya ziyarci Abonanan Takarar sa da suka kara a zaɓen da suka haɗa da Wike, da Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki, da Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Anyim Pius da sauran ƴan Takara.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy