- Advertisement -

Furodusa Isma’il FKD ya zama angon A’isha Umar

0

Furodusa Isma’il FKD ya zama angon A’isha Umar

Ango Isma’il FKD a tsakiyar wasu daga cikin abokan sana’ar sa

- Advertisement -

A YAU Juma’a, 24 ga Yuni, 2022 aka ɗaura auren matashin furodusa Isma’il Usman, wanda aka fi sani da suna Isma’il FKD, da sahibar sa A’isha Umar.

An ɗaura auren da misalin ƙarfe 2:25 na rana, bayan idar da sallar Juma’a a masallacin Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da ke Tudun Wada, Kaduna, a kan sadaki N100,000.

‘Yan fim da su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Ibrahim Al-Imash, Sabi’u M. Gidaje, Abdullahi Abu Uku, Yusuf Waza-Waza, Haruna M. Gidaje, Aminu Haske, Aminu Jahilin Malami, Ɗanladiyo Mai Atamfa da sauran su.

- Advertisement -

Ango Isma’il FKD bayan ɗaurin auren sa da A’isha

Isma’il FKD dai ƙwararren mai haɗa takalma ne na hannu na maza da mata, har da yara. Haka kuma ya na yi wa jarumai da dama takalma, masu shaguna kuma takalman sayarwa.

Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy