Gidaje 73 sun salwanta, sakamakon mamakon ruwan sama a Katsina

0

Gidaje 73 sun salwanta, sakamakon mamakon ruwan sama a Katsina - Dimokuradiyya

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Katsina ta ce Mamakon ruwan sama ya lalata gidajen al’umma 73 a karamar hukumar Kankara jihar.

Mai magana da yawun hukumar Malam Umar Mohammed ne ya sanar da hakan a ganawarsa da manema labarai, yau Litinin.

Ya kara da cewa bayan gidajen da suka lalace sakamakon ruwan saman, akwai kuma akalla mutane 3 da suka rasa rayukan su dalilin hakan.


Download Mp3

Ya kuma an samu labarin wani iftila’i ranar 11 ga watan Yuni, shima dai ma ruwan sama kamar da bakin kwarya, wanda ya shafi mutanan Ƙanƙara, Nassarawa, da Matsiga.

Tuni dai da isar jami’an hukumar ta SEMA suka fahimci karanci magufanar ruwa me ya haifar da lamarin, wanda suka yi kira ga gwamnatin jihar kan ta samar musu da magudanan ruwa.

A karshe hukumar ta SEMA ta bukaci gwamnati ta ribanya kokarin ta wajen kara yawan kayan tallafin, da za a baiwa wadanda suka gamu da iftila’in.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy