Matasa Ina muku barka da Babbar Sallah, da fatan an yi Idi lafiya, tare kuma da walwala da annashuwa.

Hakika Allah ya karrama matasa, ya kuma ba su daraja, shi ya sa ma mutum duk tsufar sa idan ya mutu za a tashe shi a sahun matasa ‘yan shekara 30. Idan muka yi duba zuwa ga wannan zamanin, matasa sune kashin bayan komai, kuma sune sahun gaba wajen aiwatar da komai, walau aikin alkairi ko na sharri, matasa sune mafi yawan masu bada gudunmawa a cikin al’umma.

Allah ya yi wa matashi baiwa mai yawa, wanda kuma mafi yawan matasan wasu sun sani, wasu kuma sabanin hakan. Haka zalika, rayuwar matashi nada muhimmanci, kuma ko wane matashi yakamata ya san da wannan, tare kuma ta samun tarbiya mai kyau, da sanin wane aboki ya kamata ya zauna dashi.

Ba a samun matashin banza face tarbiyyar sa ya gurbata daga abokin banza, ko rashin kulawa daga iyaye, ko zama da mutumin banza. A zaman takewa, wata bincike ta nuna, mutune kala 4 ne. 

Na 1, akwai mutumin da yake da kirki amma bashi da mutunci. 

Na 2 akwai wanda ke da mutunci bashi da kirki. 

Na 3 akwai wanda yake da kirki da mutunci duka biyun.

 Yayin da shi kuma na 4 shine wanda bashi da kirki ba shi kuma da mutunci.

Mutumin da yake da kirki ba shi da mutunci, shine wanda a kodayaushe kuka hadu zai dinga maka fara’a, yana janka jikinsa, amma babu kalar zagin da bazai maka ba a bayan idonka, shine idan mu’amala ta hadaku zai yi maka cutar da baka taba tsammani ba, irin wadannan mutane akwai karya, yaudara, cin amana, zalinci, butulci, hassada da rashin cika alkawari a tattare dasu.

Na 2, shine mutumin da ba shi da kirki amma yana da mutunci, shine sau tari ake ganin fuskarsu babu walwala, idan kun hadu bai damu da yayi maka magana ba, amma fa bazai taba zaginka a bayan idonka ba, kuma idan mu’amala ta hada ku dashi zai kyautata maka fiye da yadda kake tsammani, kayi ta mamaki ashe dama wane yana da mutunci? Irin haka yana faruwa a rayuwa, kila ma kasan daya a unguwar ku ko makaran ku kodai awani wajen daban.

Mutum na 3, shine kuma wanda yake da kirki da mutunci akan same shi da faran-faran da mutane, bazai taba cutar dakai a bayan idonka ba, idan mu’amala ta hada ku zai kyautata maka iyakar iyawarsa, kowa na son alaka dashi, kuma zaka sameshi da saukin Kai, ba yi da fadin Rai koda ya kasance mai shekaru, kudi, sarauta ko Kuma dai wani abun na daban.

Mutum na 4 shine, wanda bashi da kirki ba mutunci, shine wanda bai da ba ya yi wa jama’a raha, mai raina mutane, wanda sam bai iya magana ba, mutakabbiri, mahassadi, macuci, azzalimi, dan son zuciya, wanda kowa yayi mu’amala dashi sai ya cutar dashi, akwai ire-irensu a rayuwar nan, kila shima ka iya sanin daya, sakamakon mu’amala da kake da mutane.

Abokantaka ita ce haduwa ta Ruhi da kuma tunani wacce take hada tsakanin mutane da kuma haifar da ji a jika, da kuma tausasawa tsakaninsu. Yana daga cikin tilas a rayuwa, mutum ya zabawa kansa abokin hulda, wanda zai rinka nusar da shi da tunatar da shi a duk lokacin da ya shagala ko ya manta. Wanda kuma zai rinka sanar da shi abin da ya jahilta. A bisa ga dabi’ar mutum, yana son birnanci, kuma ba ya so ya kasance shi kadai a rayuwar shi. Don haka ya zama masa tilas ya samu wanda zai gudanar da rayuwarsa tare. 

Wanda zai rinka debe masa kewa, haka zalika yake jin kamar ya zamar masa dole ya sami taimakekeniya a tsakaninsa da wani, kamar yadda ya zamar masa dole ya yi hulda tare da wasu.

Abokai da abokantaka ba sabon abu bane a tarihin dan Adam, tun farko-farko

kafin yaro ya koyi magana, yakan fara kaunar yaran da suke tare da shi a cikin gida. Yakan saba dasu, yayi wasa tare da su, sannan ya kulla abota dasu.

Wani malami yana cewa, “idan ka kasance a cikin mutane, to ka yi abota da zababben su, kada ka yi abota da halakakke sai ku halaka tare”. Idan kana so ka san waye mutum, to ka tambayi abokinsa, saboda kowanne aboki da abokinsa yake koyi.

Wani kuma yana cewa, “Kar ka abota da malalaci a kowanne hali, da yawa mutumin kirki yana lalacewa ne idan ya hadu da marasa kirki. Dakiki yana saurin tasiri akan mai kokari, kamar misalin garwashi idan aka saka shi a toka shi ma sai ya zama toka.”

Hakika abokin mutum yana nuni ne da irin yanayinsa, a duk lokacin da mutane suka san yanayin abokin mutum, to sun san yanayinsa, haka nan ma a duk lokacin da suka san yanayin mutum, to sun san yanayin abokinsa.

Masu iya magana sukan ce “abokin barawo, barawo ne”. Kuma abokin mutum, abokinsa ne cikin tunani, don kuwa mutum yana koyi da mutanen da yake tare da su cikin halaye da tunani ne. Kuma a kodayaushe akan gane mutum ne da abokin huldarsa. Kamar yadda wani mawaki yake cewa, “Idan kana son ka san mutum to kalli abokinsa, duk aboki da abokinsa yake koyi. Idan abokin sharri ne to maza ka janye daga gare shi, idan kuwa na kirki ne to ka matse shi, sai ka shiriya.

Tabbass aboki yana taka rawar gani wajen canza dabi’u, halayya ko tunanin abokin zaman sa. Sau da yawa ana samun mutum ya rikide ya koma irin yadda abokin sa yake. Ta bangaren koyi da ra’ayinsa, wajen kwaikwayon maganar sa, tafiyar sa, kalar abincin da yake ci, kalar suturarsa da Kuma yadda yake sanyawa, da Kuma salo da yadda yake gudanar da rayuwarsa (lifestyle).

Babu wani wanda mutum yafi shakuwa dasu sama da iyayensa, ya kan share tsawan lokaci tare dasu, ya Kuma fada masu dukkan sirrikansa kamar abokansa. In kuwa hakane, Hakika wannan yana nuna mana muhimmancin tsayuwa haikan wajen zaban aboki da mutum zai kasance tare da shi a rayuwarsa. Saboda mahimmanci da tasiri da aboki yake dashi kan abokinsa, Annabin Allah (S) yace, “mutum yana kan addinin abokinsa (masoyinsa), kowane dayan ku ya duba wanene zai yi abokantaka dashi”. Idan kana da abokan kirki, za ka ji dadi, amma samun abokai na kwarai bai da sauki. Tabbass ko tantama babu kafin ka samu aboki na gari, dole kaima sai ka kasance nagari.

A kodayaushe mai hankali yana gujewa miyagun abokai, kamar yadda yake gujewa zaki saboda ya san babu Alkairi a tare da shi.

Abokin kwarai shi ne mai nunama kabi hanyar Allah kakuma kiyayi sabawa Allah. Aboki na gari shine wanda bazai cutar da kai ba, kuma ba zai bari acuce ka ba. In yaga za’a cuceka sai inda karfinsa ya kare, shine wanda inyaga kayi kuskure zai fadama kuskurenka, domin ka gyara, shine mai taimakonka a fannin karatunka ko Kuma sana’arka. Haka zalika shine wanda yake son cigabanka, yake baka shawara tagari, wanda baya hassada da Kai haka zalika yake fadamaka gaskiya a kowane hali sannan kuma yake so rayuwarka ta haskaka.

Idan kana da irin wannan abokin to rike shi a jikinka, kada ka bari ko jayayya ta shiga tsakanin ku da shi balle wani abu ya raba ku, domin kuwa idan ka rasa shi, wani abu ne mawuyaci ka sake samu.

Ba gwaninta bane yin abokanai dubu a shekara ba, kuma ba abin alfahari bane tara dubbanin abokanai na banza, gwaninta itace ka wadatar da abokinka a shekara dubu. Tabbas da abokai dubu na banza gwara Aboki daya tak na gari domin amfanin da zai maka a rayuwarka wadannan tarin abokan banzan bazasu iya maka ba.

Aboki nagari kamar misalin bishiya ne, idan ka zauna, karkashinta zata lullube ka da inuwarta, kuma idan ka ciri ‘ya’yanta zasu kosar da kai, idan kuma bata amfanar da kai ba, toh ba zata cutar da kai ba. Wannan magana yayi dai-dai da Hadisin Manzon Allah (SAW) da yake cewa, “Misalin aboki na gari da kuma mummunan abokin zama, kamar mai dauke da turare ne, da kuma mai hura wuta da zuga-zugi, shi mai dauke da turare kodai ya baka ka shafa, ko kuma ka saya ka shafa, ko ka amfana da kamshin sa mai dadi (yayin da iska ta doko shi zuwa hancin ka), amma shi mai zuga

wuta, ko dai ya kona maka kaya yayin da iska ta huru wutar zuwa jikinka, ko kuma ta kawo maka sakon zafi”.

Me malamai suka ce game da abokoki na gari?

Sannan menene matsayin wanda ya hada dan uwan taka da wani saboda Allah a ranar Al-kiyama?

Ku Tura Zuwa Facebook WhatsApp Twitter Instagram Da Telegram.