- Advertisement -

Gwamna Ganduje ya amince da sakin naira Miliyan 33, ga daliban jihar dake karatu a Faransa

0

Gwamna Ganduje ya amince da sakin naira Miliyan 33, ga daliban jihar dake karatu a Faransa - Dimokuradiyya

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amsa nace da sakin kudi Naira miliyan 33, a matsayin alawus ga daliban jihar, wadanda ke karatun digirin farko a jami’o’i daban daban dake ƙasar Faransa.

- Advertisement -

Kwamishinar ilimi mai zurfi ta jihar Kano Dakta Mariya Mahmoud Bunkure ce ya bayyana hakan, a cikin wata Sanarwa da aka rabawa manema labarai yau Lahadi.

Mariya ta kara da cewa wannan kason wani bangare na tallafin da gwamnatin Kano, ta kuduri aniyar aiwatar ga daliban Kano dake karatu a Faransa, karkashin wani shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Kano da kasar Faransa.

Wannan tallafin dai an bayar da shi ne ga daliban, wadanda suke karatun kimiyya da fasaha, a can ƙasar, da nufin idan sun kammala sun dawo, jihar Kano tayi alfahari da su.

- Advertisement -

Sanarwar ta kara da cewa karkashin wannan shiri, malamai da dama a manyan makarantun gaba da sikandire a jihar sun Amfana, da samun digiri na biyu, da kuma na uku.

Kazalika wasu daga cikin tuni sun kammala sun dawo jihar Kano, yayin da wasu ke a shekarar karshe don kammalawa, kuma suma zasu dawo jihar Kano, don ci gaba da tallafawa bunƙasar jihar.

- Advertisement -
wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy