- Advertisement -

Gwamna Ganduje Ya fadi dalilin rashin Karbar bakuncin sarkin Kano a hawan Nassarawa

0

Gwamna Ganduje Ya fadi dalilin rashin Karbar bakuncin sarkin Kano a hawan Nassarawa - Dimokuradiyya

Gwamnatin jihar Kano ta ce wani muhimmin taro na gwamnonin kasar nan da Ganduje ya halarta a Abuje ne dalilin da ya sanya bai karbi sarkin Kano a Hawan Nassrawa ba.

- Advertisement -

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammadu Garba ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Ya ce taron da gwamnan ya tafi babu makawa sai yaje da kansa, kana daga bisani ya wuce ya yiwa shugaba Muhammadu Buhari bayani kan taron.

Muhammad Garba ya ce wadanda ya kamata su karbi gwamnan a madadinsa su ne mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna da kuma kakakin Majalisar Kano Ibrahim Chidari wanda yanzu haka duk suna kasa mai tsarki.

- Advertisement -

Haka kuma mutum na uku da ya Kamata ya karbi sarki shi ne sakataren gwamnati Alhaji Usman Alhaji wanda shi kuma hakimi ne a masarautar Gaya, da ake ganin ba a girmama sarkin ba idan aka ce ya karbe shi.

Sanarwar ta kara da cewa sai da gwamnan ya tattauna da Sarkin kan halin da aka tsinci kai ya kuma baiwa sarkin damar ya yi Hawan ya kewaya Inda aka saba bi don gaisawa da jama’a.

A don haka ya bukaci jama’a da su yi watsi da jita jitar da ake yadawa cewa gwamnan da gangan ya ki karbar sarkin

- Advertisement -

Inda ya ce kafin wannan al’amari ya faru gwamnan ya gaisa da Sarkin a Masallacin Ida da gidan Shattima ya kuma je Hawan Daushe da hakan ke nuna babu matsala.

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy