- Advertisement -

Gwamna Ganduje Yace Tinubu Ba Dan Takara Bane Na Gwaji

0

Gwamna Ganduje Yace Tinubu Ba Dan Takara Bane Na Gwaji - Dimokuradiyya

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai dan takarar shugaban kasa, wanda ba shugaba ne na gwaji ba duba da irin kwazonsa da kafuwar sa a harkokin siyasa da gudanar da ayyuka a Najeriya.

- Advertisement -

Gwamnan ya bayyana hakan ne a masaukin Gwamnan da ke Gidan Aminu Kano, a Abuja, lokacin da ya karbi lambar yabo da kungiyar hadin kan Tinubu Support Groups Worldwide, na ‘National Directorate’ wato daraktan kungiyar na kasa, da suka hada da Najeriya, Amurka, burtaniya, Canada, Ireland suka ba shi lambar yabo. Kasashen Jamus, Afirka ta Kudu, Saudi Arabia, Brazil, Oman, da UAE, saboda rawar da ya taka wajen nasarar Tinubu a zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Wannan na kunshe ne a ciki wata sanar da kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba ya aikewa Dimokuradiyya; Ya ce ganin yadda ya yi fice a matsayinsa na gwamnan jihar Legas inda ya kafa wata gaggarumar tawaga da ta kunshi mutane daga sassa daban-daban na kasar nan wadanda suka mayar da jihar zuwa mafi karfin tattalin arziki a shiyyar, shugabancin Asiwaju zai iya tafiyar da al’amuranmu da dama.

Ganduje ya yi nuni da cewa fitowar Asiwaju a zaben fidda gwani na ba da fata da kwarin gwiwar cewa jam’iyyar ta shirya yin nasara a zaben 2023.

- Advertisement -

Gwamnan ya kuma godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa samar da yanayin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da gwamnoninta da kuma sauran masu neman takara da suka bayyana a shirye suke su hada kai da Asiwaju domin samun nasarar jam’iyyar.

Sanarwar ta kuma ce, Ya nuna jin dadinsa da karramawar da kungiyar ta yi masa, ya kuma yi alkawarin kara yin aiki tukuru domin samun nasarar takarar shugaban kasa na Asiwaju.

Tun da farko, Babban Darakta Janar na kungiyar, Dakta Doyin Johnson, ya bayyana cewa an ba Gwamna Ganduje lambar yabon ne a matsayin godiya ga dabarar rawar da ya taka wajen tabbatar da shugabancin Asiwaju.

- Advertisement -

Ya kuma roki gwamnan da ya ci gaba da yin amfani da basirarsa da kuma kwazonsa na gangami domin tabbatar da nasarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben mai zuwa.

Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shima da yake nasa jawabin, gwamnan jihar Imo, wanda yana cikin tawagar, ya dorawa gwamnan da ya bayyana a matsayin mutum mai daraja, da ya kara tsara dabarun cin zabe a karo na biyu a shekarar 2023.

- Advertisement -
wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy