- Advertisement -

Gwamna Matawalle Ya Goyi Bayan Hukuncin Kisa Ga ‘Yan Bindiga, Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar

0

Gwamna Matawalle Ya Goyi Bayan Hukuncin Kisa Ga ‘Yan Bindiga, Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar - Dimokuradiyya

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya amince da hukuncin kisa kan wadanda aka samu da laifin yin fashi da makami da garkuwa da mutane da satar shanu da kuma kungiyoyin asiri a jihar.

- Advertisement -

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan sanya hannu kan dokar da Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta zartar na haramtawa tare da hukunta ‘yan ta’adda, satar shanu, kungiyoyin asiri, garkuwa da mutane da sauran laifukan da suka faru.

Matawalle ya kara da cewa, a karkashin dokar, duk wanda aka samu da hannu a cikin wadannan laifuffukan da aka ambata, yana da hukuncin daurin rai-da-rai ko daurin shekaru ashirin ko daurin shekaru goma a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin sa ta shirya tsaf domin yakar masu aikata miyagun laifuka a jihar a cikin tsarin doka don tabbatar da zaman lafiya a jihar, musamman a al’ummomin da ake daukar su a matsayin cibiyar ‘yan bindiga.

- Advertisement -

“Sabuwar dokar ta tanadi cewa duk mutumin da aka samu da laifin aikata fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu, bangaranci ko kuma zama mai ba da labari ga barayin, yana da hukuncin kisa.

“A karkashin doka, duk wanda aka samu da hannu wajen taimakawa ko kuma aikata laifukan da aka ambata, yana da hukuncin daurin rai-da-rai, daurin shekaru ashirin ko kuma daurin shekaru goma ba tare da zabin biyan tara ba.

“Babban abin da ya fi mayar da hankali kan mulki a ko’ina a duniya shine tsaro,” in ji shi.

- Advertisement -

Gwamna Matawalle ya bayyana cewa jami’an tsaron da aka kafa bai bambanta da rundunar hadin gwiwa ta Civilian Task Force, JTF a jihar Borno da kuma Amotekun a yankin Kudu-maso-Yamma ba.

Yayin da ya yaba wa Majalisar Dokokin Jihar bisa yadda tsarin mulki ya ba su na samar da dokoki don tabbatar da zaman lafiya a Jihar, ya kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa irin goyon bayan da take baiwa Jihar Zamfara.

Tun da farko kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Hon. Nasiru Magarya ya ce dokar za ta zama makami na shari’a don hukunta masu aikata laifin fashi a jihar.

- Advertisement -

Shima da yake tsokaci, shugaban kwamitin majalisar akan ayyukan ta’addanci da laifuka, Hon. Abdullahi Shinkafi ya gargadi masu tayar da kayar baya da masu garkuwa da mutane da su daina yin hakan.

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy