- Advertisement -

Gwamna Zulum ya ƙaddamar da hanyar cikin gari, Asibiti

0

Gwamna Zulum ya ƙaddamar da hanyar cikin gari, Asibiti - Dimokuradiyya

Gwamna Zulum ya ƙaddamar da hanyar ciki, Asibiti

- Advertisement -

Gwamnan Jahar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ƙaddamar da hanyar cikin gari mai kilomita 2.17 tare da Magudanan Ruwa a cikin garin Maiduguri.

Sabuwar hanyar ta fara daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ramat akan hanyar Maiduguri zuwa Filin jirgi zuwa Wulari, Inda ta samar da hanya ga Al ummar Wulari da Cibiyar Maiduguri.

Gwamnan ya kuma ƙaddamar da Cibiyar kula da lafiya a matakin farko mai gadaje 30, da aka gina a yankin da yayi ƙaurin suna wajen Karuwanci da sauran wasu aikace-aikacen ta’addanci.

- Advertisement -

Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar an gudanar da aikin ne a lokacin da Gwamnan ya ziyarci wurin, inda aka gano cewa wurin matattarar ƴan ta’adda ne.

Asibitin wanda aka katange, yana da ɓangare guda biyu dana maza da Mata, da kayayyakin gwaje-gwaje, da Solar da kuma ruwa.

Da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da ayyukan, Zulum yace abinda ya rage shine Jami’an Ma’aikatar Lafiya su tabbatar da samar da ingantacciyar lafiya ga ƴan ƙasa an bada ta, ta hanyar samar da kayayyakin gwaje-gwaje da Likitoci, Malaman Unguwar zoma, da Ma’aikatan Lafiya.

- Advertisement -

Bayan ya ƙaddamar da hanyar Wulari da Asibitin, Zulum ya ƙaddamar tare da bada umarnin bada magungunan mata da yawan su yakai Miliyan 300 a cibiyoyin lafiya a faɗin jahar

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy