Gwamnatin Imo Ta Musanta Rade-radin Da Akeyi Na Mutuwar Gwamna Uzodinma
Gwamnatin jihar Imo ta mayar da martani game da rade-radin mutuwar gwamna Hope Uzodinma, inda ta bayyana hakan a matsayin rashin tushe, kuma karya ce mara hankali.
An wallafa wani sakon faifan murya da aka nada a shafukan sada zumunta inda aka ce gwamnan ya yi fama da bugun jini kuma an garzaya da shi zuwa kasar Indiya domin yi masa magani amma bai samu ba.
Sai dai Kwamishinan Yada Labarai da Dabaru na jihar, Declan Emelumba, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce gwamnan “ba wai kawai yana da hazaka ba amma yana matukar halartar duk wasu ayyukan da ya tsara a Abuja babban birnin kasar.”
Ya ce Uzodinma ba shi da wani kalubale da zai kai ga bugun jini.
“Gwamnan ya halarci taro da shugaban kasa tare da wasu gwamnonin APC a safiyar yau. Da nake magana, ya shiga wani taron jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki gabanin babban taron jam’iyyar APC.
“Don haka ban san ainihin abin da masu yada wannan jita-jita ke son cimma ba,” in ji Emelumba.
