- Advertisement -

Gwamnatin Kano Ta Samar Da Wani Kwamiti Don Duba Al’amuran Hukumar Hisbah

0

Gwamnatin Kano Ta Samar Da Wani Kwamiti Don Duba Al’amuran Hukumar Hisbah - Dimokuradiyya

Gwamnatin jihar Kano ta amince da samar da kwamitin gudanarwar hukumar Hisba ta jihar Kano.

- Advertisement -

Kwamitin dai yana dauke mutane 22, wadanda zasu yi aiki tare, don duba kan harkokin hukumar tare da bayar da shawarwari lokaci zuwa lokaci.

Kwamishinan yada labarai na Kano Muhammad Garba ne ya sanar da hakan ga manema labarai, inda yace kwamitin zai kuma sake yin duba kan yadda hukumar take gudanar da ayyukan ta.

Ya ce tuni aka ƙaddamar da kwamitin, sannan zai tattara rahoton sa na farko tare da gabatar da shi gaban majalisar zartarwa ta jihar Kano.

- Advertisement -

Tuni aka naɗa Sheik Ibrahim Shehu Maihula a matsayin shugaban kwamitin.

Daga cikin mambobin kuwa akwai shugaban hukumar Hisbah Sheik Harun Ibn Sina, da wakilan hukumar a masarautu 4 na jihar Kano, da wakilai daga rundunonin tsaro na jihar baki daya.

- Advertisement -
wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy