Gwamnatin Kano ta zabi kamfanin jirgin sama daya tilo, don jigilan alhazan jihar

0

Gwamnatin Kano ta zabi kamfanin jirgin sama daya tilo, don jigilan alhazan jihar - Dimokuradiyya

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa jirgin Max Air ne zai yi jigilar Alhazanta zuwa kasa mai tsarki a bana.

Babban sakataren hukumar Jin dadin Alhazai na Kano Muhammad Abba Dambatta ne ya tabbatar da hakan yayin taron manema Labarai yau Lahadi.

Ya ce bayan dogon nazari da tattaunawa da masu ruwa da tsaki yanzu an tabbatar da Jirgin Max Air a matsayin wanda zai yi jigilar alhazan Kano, duk da tarin kamfanonin da suka nemi makamanciyar wannan dama.


Download Mp3

Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata ne dai Kamfanin Azman Air ya ce hukumar jin dadin alhazai ta kasa NAHCON ta bashi damar ya yi jigilar Alhazan Kano.

Sai dai hukumar Jin dadin Alhazai ta Kano ta ki amincewa da baiwa Kamfanin dama.

Duk kuwa da cewa kamfanin mallakin dan Kano ne, kuma da dama cikin Ma’aikatan kamfanin yan Kano ne.

Inda ta ce Shekara da shekaru ta na aiki ne da Kamfanin Max Air kuma bai taba Basu matsala ba, babu dalilin da zai sa su yi watsi da shi.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy