- Advertisement -

Gwamnatin Tarayya zata ɗauki ƴan Najeriya Miliyan 1 aikin Ƙidayar Al’umma ta 2023 — NPC

0

Gwamnatin Tarayya zata ɗauki ƴan Najeriya Miliyan 1 aikin Ƙidayar Al’umma ta 2023 — NPC - Dimokuradiyya

Gwamnatin Tarayya zata ɗauki ƴan Najeriya Miliyan 1 aikin Ƙidayar Al’umma ta 2023 — NPC

- Advertisement -

Hukumar Ƙidayar Al’umma ta Kasa NPC tace kimanin ƴan Najeriya Miliyan ɗaya, Gwamnatin Tarayya zata ɗauka aiki domin su gudanar da aikin Ƙidayar Al’umma a Shekarar 2023.

Hukumar ta bada tabbacin cewa ingantattun fasahohi NPC za tayi amfani dasu domin gudanar da ɗaukar masu ƙidayar, domin magance ƴan siyasa ko wasu manya daga hana gudanar da shirin.

Kwamishina mai Wakiltar Jahar Ekiti a Hukumar NPC Mr Deji Ajayi ya bayyana haka a Ado Ekiti, a jiya, a wani taron Manema Labaru akan wani shirin ƙidaya, domin shirin ƙidaya na Shekara mai zuwa.

- Advertisement -

Tsohon shugaban Ma’aikatan Jahar Ekiti ya ƙara dacewa garuruwa guda tara a cikin Ƙananan Hukumomi 9, daga cikin guda 16 a Jahar, an zaɓe su domin shirin shata gundumomin, don sauƙaƙa aiki.

Yayi nuni dacewar yankunan da za’a ƙidaya a shirin ƙidaya na Trial Census ya ƙunshi Ado, sa Emure, da Iro, da Ijero, da Ikole, da Iworoko, da Ise, da Ikun, da Omuo Ekiti.

Da yake bayyana mahimmancin kidaya ga cigaban ƙasa, Ajayi yace ƙididdigar Al’umma, Kamfanoni zasu yi amfani dashi domin tsara yadda za’a ɗauki ƴan Najeriya aiki, ta hanyar sanin yawan su.

- Advertisement -

“Gwamnati za tayi amfani da wannan ƙididdigar Al’umma domin shirya wa matasa, Ɗalibai, da lafiyar da ake bukata.

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy