Gwamnoni sun miƙa sunayen Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa 5 ga Buhari, an cire Ahmed Lawan daga ciki

0

Gwamnoni sun miƙa sunayen Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa 5 ga Buhari, an cire Ahmed Lawan daga ciki - Dimokuradiyya

Yanzu-Yanzu: Gwamnoni sun miƙa sunayen Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa 5 ga Buhari

Gwamnoni wanda suna daga cikin mambobin Jam’iyyar APC sun miƙa sunayen Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa 5 ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari domin ya zaɓi Ɗan Takara, kamar yadda Daily Trust ta tabbatar daga majiya mai tushe a safiyar nan.

Wata majiya mai ƙarfi ta shaida cewa Gwamnonin sun mika sunayen da sanyin safiyar yau Talata.

Sunayen kamar yadda Majiyar ta tabbatar sun ƙunshi Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, da tsohon Gwamnan Jahar Lagos Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da Gwamna Kayode Fayemi (Jahar Ekiti) da Rotimi Amaechi tsohon Ministan Sufuri, da Gwamna Dave Umahi na Jahar Ebonyi.


Download Mp3

Kamar yadda Jaridar Dimokuraɗiyya ta gano, Gwamnonin bayan taron su da Shugaban Ƙasa sun ce zasu dawo Villa, bayan sun yi taro da Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar, da sauran masu ruwa da tsaki.

“”Sun ɗauko mutum ɗaya daga yankin Kudu Maso Gabas, da Kudu maso Kudu, da kuma guda uku daga yankin Kudu maso Yamma, wanda ƙudirin su yayi dai-dai da buƙatar maida mulki zuwa Kudu,” Inji shi.

Yace ana saran Shugaban Ƙasa zai zaɓi mutum guda daga jerin sunayen.

Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta gano cewa, Zaɓen Fidda Gwani na Shugaban Ƙasa zai gudana a yau. shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan wanda Shugaban Jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya sanar cewa shine aka fitar a matsayin Ɗan Takara ta hanyar Sasanci an fitar da sunan sa.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy