- Advertisement -

Gwamnonin APC Uku Sun Yi Ganawar Sirri Da Wike

0

Gwamnonin APC Uku Sun Yi Ganawar Sirri Da Wike - Dimokuradiyya

A yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar a jam’iyyar PDP, gwamnoni uku da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC na ganawa da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

- Advertisement -

A ranar Juma’a ne Wike ya karbi bakuncin Gwamnonin Legas, Babajide Sanwo-Olu, Jihar Ekiti wanda kuma ya hada da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi da takwaransa na Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Wike ya kuma hadu da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose domin tarbar gwamnonin.

Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa gwamnonin sun shiga ganawar sirri da Wike.

- Advertisement -

Wasu majiyoyi na kusa da gwamnan jihar Ribas sun yi nuni da cewa watakila hakan ba zai rasa nasaba da zaben shugaban kasa na 2023 ba.

Ku tuna cewa Wike ya ji takaicin yadda dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya zabi gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa.

A Wani Labarin Kuma Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta tabbatar da rasuwar wata mahajjaciya Hasiya Aminu, daga cikin tawagar alhazan jihar Kaduna.

- Advertisement -

Ta rasu ne a cikin barcin da take yi jim kadan bayan ta dawo daga dutsen Arafat, kamar yadda makwabtanta a cikin tanti suka bayyana.

Dokta Usman Galadima, babban jami’in aiyuka kuma shugaban ma’aikatan lafiya na Najeriya, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa har yanzu ba a tantance dalilin mutuwar ta ba.

Ya ce tuni aka sanar da iyalan Aminu rasuwarta kuma za a yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

- Advertisement -

Hasiya Aminu itace ne mahajjaciya ta biyu da ta rasu a aikin Hajjin bana 2022.

Hajiya Aisha Ahmed daga Keffi a jihar Nasarawa ita ma ta rasu a makon jiya bayan gajeriyar rashin lafiya kuma an yi jana’izarta a Makkah.

Zaman Arafa a tsawon yini ya zama wajibi ga kowane mahajjaci ya cika domin yin aikin Hajji.

- Advertisement -

Alhazan Najeriya daga cikin sama da miliyan daya da ke aikin Hajjin shekarar 2022 a Arafat.

Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Arafat dai ita ce wurin da Annabi Muhammad S.A.W ya gabatar da hudubarsa ta karshe ranar Juma’a kafin rasuwarsa.

- Advertisement -
wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy