Gwamnonin Arewa sun murƙushe damar Atiku na zama Shugaban Ƙasa — Cewar DG VON

0

Gwamnonin Arewa sun murƙushe damar Atiku na zama Shugaban Ƙasa — Cewar DG VON - Dimokuradiyya

Gwamnonin Arewa sun murƙushe damar Atiku na zama Shugaban Ƙasa — Cewar DG VON

Wani Jigo a Jam’iyyar APC Osita Okechukwu ya jinjinawa Gwamnoni 10 na Arewa bisa goyon bayan miƙa takarar Shugaban Ƙasa zuwa yankin Kudu.

A lokacin da yake bayyana abinda suka yi a matsayin kishi, Darakta-Janar na Muryan Afirka ta Najeriya VON yace hakan yafi girma ma Daloli domin samun nasara, musamman na Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na PDP Atiku Abubakar daya nuna a lokacin zabe.

Okechukwu Wanda ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, ya taya murna ga Gwamnonin Arewa da Shuwagabannin Siyasa da suka inganta haɗin kan Najeriya, ta hanyar goyon bayan miƙa ragamar mulki zuwa Kudu.


Download Mp3

Yace “Najeriya yanzu taga ruwan Daloli, daya fito da Alhaji Atiku Abubakar a matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na PDP, wanda ya nuna cewa bashi da komai a ajiye ga mafarkin samun sabuwar Najeriya.

“Na yarda cewa nasarar Atiku, ba zata haifar da Nasara ba, musamman kishin da ƴan uwansa ƴan Arewa suka nuna”.

Shugaban VON yace PDP bawai ta karya Kundin Tsarin Mulkin ta ba, amma ta binne ta siyasar ta a Zaɓen Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023.

Yace matsayar mika ragamar mulki zuwa yankin Kudu, Shuwagabannin Arewa sun tabbatar da Son cigaban APC, Kuma sun hana damar PDP.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy