- Advertisement -

Hanyoyin sadarwar kasar Canada sun gamu da wani Cikas

0

Hanyoyin sadarwar kasar Canada sun gamu da wani Cikas - Dimokuradiyya

Karancin yanayin sadarwa mai kyau ya shafi hanyoyin sadarwar wayar hannu da Intanet a kasar Canada.

- Advertisement -

Lamarin dai ya faru ne bayan babban kamfanin kula da yanayin sadarwar kasar, ya tabbatar da gamuwa da tsaiko, tun a ranar juma’ar data gabata.

Lamarin dai yanzu haka ya kawo cikas ga harkokin banki, kira, biyan kudi da ma harkokin gudanarwa a sassa daban daban.

Kamfanin sadarwa na Rogers ya ba da rahoton ci gaba a cikin wannan rana, yana mai cewa “ayyukan da suke sha kansu yanzu haka sun fara warwarewa.”

- Advertisement -

Kashi ɗaya cikin huɗu na haɗin Intanet na kasar Kanada ne ya gamu da lalacewa, a cewar bayanai daga NetBlocks, ƙungiyar sa ido kan harkokin Intanet.

Rogers shine babban kamfanin da aka koma amfani da shi ga wayar hannu a kasar, tare da masu biyan kuɗi sama da miliyan 11 da masu amfani da Intanet kusan miliyan uku – tare da haɗin gwiwa tare da Bell Inc.

Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin da ya jawo katsewar ba.

- Advertisement -

Evan Koronewski, mai magana da yawun Hukumar Tsaro ta Sadarwa, wata hukumar gwamnati da ke da alhakin tsaro ta yanar gizo da bayanan sirri, ya shaida wa AFP cewa “a wannan lokacin, CSE ba ta da wata alama cewa wannan yana da alaƙa da mummunar barazanar yanar gizo ba.”

Ministan masana’antu Francois-Philippe Champagne ya ce ya yi magana da Shugaban Kamfanin Rogers kuma ya bashi tabbacin kawo karshen karancin matsalar sadarwar.

- Advertisement -
wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy