Harin Cocin Owo: Bai Kamata A Ci Zarafin ’Yan Arewa Mazauna Kudu Ba – Shehu Sani

0

Harin Cocin Owo: Bai Kamata A Ci Zarafin ’Yan Arewa Mazauna Kudu Ba – Shehu Sani - Dimokuradiyya

Biyo bayan wani mummunan hari da wasu ‘yan ta’adda suka kai wa mabiya Coci a garin Owo na jihar Ondo, tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi gargadi kan cin mutuncin ‘yan Arewa mazauna Kudu.

Shehu Sani ya yi wannan gargadin ne a ranar Litinin a shafinsa na Twitter, inda ya ce manufar ‘yan ta’addar ita ce ta haifar da barna da rigingimun kasa.

“Ba sa barin masu ibada a cikin masallatai ko a coci-coci. Arewa ce ke fama da tashe-tashen hankula a kullum,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Sai dai a baya Sanata Shehu Sani ya yi Allah-wadai da harin da aka kai a cocin Katolika na Ondo, yana mai bayyana hakan a matsayin wani mummunan aiki na ta’addanci, da dabbanci da kuma abin la’akari.

“Dole ne dukkan ‘yan Najeriya su hada kai wajen yin tir da wadanda suka aikata wannan danyen aikin.

Dole ne a yi duk abin da za a gabatar da maharan. Ya isa wannan zubar da jini,” ya rubuta.


Download Mp3

Al’amarin da ya faru a Cocin Owo, wanda shi ne hari na baya-bayan nan a Najeriya, na ci gaba da yin tofin Allah tsine daga ciki da wajen kasar, inda ake ta kiraye-kirayen hukumomi da su yi abin da ya kamata wajen kare martabar rayuka.

A WANI LABARIN KUMA

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai hari a ranar Asabar a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce adadin wadanda aka yi garkuwa sun kai sama da mutane hamsin yayin da aka hallaka wata mace guda daya.

Sai dai har yanzu rundunar ‘yan sandan ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba, sama da sa’o’i 24 bayan kisan gillar da aka yi, kamar yadda wasu kiraye-kirayen da aka yi wa rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato, PPRO, Abubakar Sanusi, bai amsa ba, haka kuma bai amsa sakon tes da aka aika masa ba.

Wata majiya da ta so a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa an kashe matar wani Dagacin kauye tare da yin garkuwa da mutane da dama a wani daurin aure da aka yi a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto a yammacin ranar Asabar.

A cewar majiyar, “’yan bindigar sun ja hankalin mahalarta babban taron baki daga garuruwa masu nisa da na kusa da su zuwa Gebe. Matar shugaban kauyen ita kadai aka kashe saboda ta ki yarda a sace ta.

“ Ita kadai ce aka kashe kamar yadda na sani lokacin da ta tsaya tsayin daka cewa ba za ta bi ‘yan bindigar zuwa maboyarsu ba.

“Baya ga wadanda aka yi garkuwa da su aka tafi da su zuwa wuraren da ba a san ko inane ba, wasu da dama sun samu raunuka a kokarinsu na tserewa daga sace su.”

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy