Hira Da Mahaifiyar Nura Mustapha Kan Rasuwarsa
Abin Tausayi! Mahaifiyar Marigayi Nura Mustapha Ta Bayyana Sanadiyyar Rasuwar Yaron Nata Da Irin Babban Rashin Da Tayi, Masana’antar KannyWood Ta Girgiza Sosai Da Rasuwar Daraktan Shirin IZZAR SO, Nura Mustapha Waye, Inda Mutuwar Tashi Ba Iya Iyalansa Da Yan Uwansa Akayi Ba. Har Masana’antar KannyWood Suma Wannan Rashin Ya Jijjigasu.
Nura Mustapha Ya Rasu Ne Ranar Lahadi Uku Ga Watan Bakwai Na Shekarar Dubu Biyu Da Ashirin Da Biyu. Inda Ya Rasu Da Misalin Karfe Goma Sha Daya.
Mahaifiyarsa Da Wasu Jaruman Masana’antar KannyWood Sun Bayyana Yadda Suji Mutuwar Tashi, Sakamakon Mutuwar Tazo Masa Lokaci Guda. Domin Ko Labarin Rashin Lafiyasa Ba.aji Ba.
Mun Kawo Muku Sautin Murna Na Yadda Mutane Suji Bayan Mutuwar Daraktan. Mamacin Ya Samu Sheda Sosai Domin Kuwa Ya Zauna Da Kowa Lafiya Kalau, Kuma Masoyine Na Annabi Muhammad S.A.W.
