Hotuna: Hukumar Kula Da Ababen Hawa Ta Jihar Legas Ta Murkushe Baburan Masu Okada 2,228

0

Hotuna: Hukumar Kula Da Ababen Hawa Ta Jihar Legas Ta Murkushe Baburan Masu Okada 2,228 Da Ta Damke - Dimokuradiyya

Hukumar kula da ababen hawa ta jihar Legas ta sake murkushe wasu baburan kasuwanci 2,228 da aka kama wanda aka fi sani da Okada a ranar Juma’a.

An kama baburan ne bayan Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya hana su gudanar da ayyukan su a kananan hukumomi shida na jihar.

Shugaban hukumar, CSP Shola Jejeloye, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa hukumar za ta kara zage damtse wajen ganin an murkushe dukkan baburan da aka kama bayan bin ka’idojin da suka dace.

Gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC da aka shirya gudanarwa tsakanin ranakun 6 zuwa 8 ga watan Yuni, jam’iyya mai mulki tace masu neman tsayawa takara shugaban kasa 10 ne basu can canta ba.

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa Shugaban Kwamitin tantance masu neman tsayawa takarar Shugaban kasa kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Cif John Oyegun ne ya bayyana haka a yau Juma’a a Abuja lokacin da ya mika rahoton kwamitin ga jam’iyyar.

Har yanzu ba a bayyana sunayen masu neman tsayawa takarar da basu can canta ba.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy