Hukumar ‘Immigration’ ta ƙara wa Jami’ai 98 manyan Muƙamai

0

Hukumar ‘Immigration’ ta ƙara wa Jami’ai 98 manyan Muƙamai - Dimokuradiyya

Hukumar ‘Immigration’ ta ƙara wa Jami’ai 98 manyan Muƙamai

Kimanin Manyan Jami’an 98 na Hukumar Hana Shige da Fice na Najeriya aka ƙara masu sabbin muƙamai, biyo bayan ƙoƙarin da suka yi a Jarabawar Ƙarin girma da aka gudanar a watan Disamba na Shekarar 2021.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da aka fitar a ranar 20 ga watan Mayu na Shekarar 2022.

A cewar Sanarwar daga Amos Okpu, Mataimakin Kwanturola Ɓangaren Kula da harkokin Hulɗa da Jama’a, takardar mai kwanan watan 28 ga watan Mayu na Shekarar 2022, ya ƙunshi yanayin yadda akayi ƙarin girman da sunayen su daya ƙunshi mutane 4 da aka ƙara masu girma zuwa Mataimakan Kwanturola-Janar, sai 24 suma an ƙara masu girma zuwa Mataimakan Kwanturola-Janar, a yayinda wasu guda 70 aka ƙara masu girma zuwa muƙamin Kwanturola na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa.

Wanda aka ƙara wa girman zuwa Mataimakan Kwanturola-Janar sun haɗa da Josephine Chisara Kwazu, da Modupe Oshoke Anyalechi, da Muhammad Aminu Muhammd da kuma Ajoke Oluremi Talabi.

Waɗanda suma aka ƙara masu matsayi zuwa ACG sun haɗa da Nandap Kemi Nanna, da Kwanturola a Filin Jirgin Saman Ikeja, Lagos Ahmed Bauchi Aliyu, da Shugaban Ma’aikatan muƙaddashin Kwanturola-Janar Abdullahi Usman Musa, da Kwanturola mai kula da Hedikwatar Hukumar Amao Kolawole Micheal, da Kwanturola na Jahar Ogun Alawode Nuratu Betty, da Kwanturola mai Kula da Jindaɗin Ma’aikata da Dai-dai to Acholonu Alphonsus, da kuma Kwanturola na Jahar Ekiti, da sauran su.

Waɗanda aka ƙara wa girma zuwa muƙamin Kwanturola sun haɗa da Adesokan Adeola, dake a Makarantar kula da horon Ma’aikata.

Sai mai kula da Harkokin Hukumar na Hedikwatar ta Kasa, da kuma biza Bagari Ahmad Dauda. Da mai kula da yin Fasfo Bewaji Abolupe Oladoyin.

Akwai kuma mai kula da Kila Liman Sani mai kula da yin Fasfo a Jahar Kano da sauran su.

Sanarwar tace muƙaddashin Kwanturola-Janar Isah Jere Idris a lokacin da yake taya su murna “yayi amfani da damar yana bayyana Jindaɗinsa ga Gwamnati data ga ya kamata a ƙara masu muƙamin. Yayi kira ga Jami’an da aka ƙara masu girma dasu cigaba da Jajircewa a muƙamin da suka samu.”

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy