Hukumar NAHCON Ta Sanar Da Farashin Kudin Aikin Hajjin Bana Ga Maniyyata

0

Hukumar NAHCON Ta Sanar Da Farashin Kudin Aikin Hajjin Bana Ga Maniyyata - Dimokuradiyya

Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayyana adadin kudin da kowace shiyyar siyasar kasar Najeriya za ta biya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2022.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Asabar, shugabar hukumar Zikirullah Kunle Hassan ya bayyana cewa kowane mahajjaci daga yankin kudancin kasar nan zai biya Naira miliyan biyu da dubu Dari hudu da casa’in da shida da dari takwas da sha biyar da kobo ashirin da tara 2,496,815.29.

Sannan tace yayin da takwarorinsa na yankin Arewacin kasar nan za su biya Naira miliyan biyu da dubu dari hudu da arba’in da tara da dari shida da bakwai da kobo tamanin da tara 2,449, 607.89.

Ya kara da cewa, “Jihohin Adamawa da Borno za su biya Naira miliyan biyu da dubu dari hudu da takwas da dari da casa’in da bakwai da kobo tamanin da tara 2, 408, 197.89 saboda kusancin da suke da shi da Saudiyya.”

Sanarwar ta kara da cewa farashin tikitin jirgin sama ne zai zama babban banbancin kudin aikin hajjin, inda ta kara da cewa maniyyatan za su biya Naira 30,000 don samun gwajin COVID-19 na PCR, wanda ya ce yana daya daga cikin sharuddan aikin.

A yayin da yake jawabi a wani taro na musamman da shugabanin hukumar jin dadin Alhazai ta yi a ranar Asabar, shugaban ya bukaci masu ruwa da tsaki da su gaggauta shiri domin babu wani abin jin dadi.

Ya kuma bukaci wasu da su tura ma’aikatansu domin yin nazari kan tsarin gudanar da bizar saboda sauye-sauyen da Saudiyya ta bullo da shi a bana.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy