Ina da tabbacin zan samu nasara, don haka bazan Janye wa Atiku, Tinubu — Kwankwaso

0

Ina da tabbacin zan samu nasara, don haka bazan Janye wa Atiku, Tinubu — Kwankwaso - Dimokuradiyya

Ina da tabbacin zan samu nasara, don haka bazan Janye wa Atiku, Tinubu — Kwankwaso

A wata tattaunawa da akayi da madugun Ƴan Kwankwasiyya kuma Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yace bazai janyewa kowa ba, koda Ɗan Takarar Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, dana APC Bola Tinubu.

Ta yaya zaka doke APC da PDP ta la’akari da sanin su da akayi a ƙasa.


Download Mp3

Kowa yasan Kwankwasiyya, zamu nasara koda a yankin Arewa maso Gabas ne. Ina farin ciki yadda aka sanya Dokar Zaɓe, wanda zaiyi wahala, wani ya yi Maguɗi a zaɓe, kamar yadda suka yi a baya.

Indai akwai zaɓe na Gaskiya, to zaiyi wahala a kada mu. A saboda haka, inada tabbaci na samun nasara akan Ɗan Takarar Jam’iyyar APC Bola Tinubu da Atiku Abubakar na PDP a babban zaɓen shekarar 2023.

A shirye kake, ka sadaukar da Takarar Shugaban Ƙasa ga Atiku, domin taimakawa wajen Kada APC a Babban Zaɓe?.

Bazan Janye wa kowa ba, kowa yasan Jam’iyyar mu a ko’ina a Ƙasar nan, kuma muna da tabbacin samun nasarar a Zaɓe.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy