INEC ta ƙaryata jita-jitar buɗe wurin rajistar Katin Zaɓe a Jamhuriyar Nijar

0

INEC ta ƙaryata jita-jitar buɗe wurin rajistar Katin Zaɓe a Jamhuriyar Nijar - Dimokuradiyya

INEC ta ƙaryata jita-jitar buɗe wurin rajistar Katin Zaɓe a Jamhuriyar NijarÏ

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta musanta batun buɗe wurin rajistar Katin Zaɓe a Jamhuriyar Nijar.

Wannan cigaba na zuwa ne bayan wata jita-jita da tayi yawo a Kafafen Sadarwa na Zamani cewa Hukumar ta fara shirin yiwa ƴan Najeriya rajista baya ga cikin Ƙasa.

Wani shafi na Facebook na wani Nche Nwabuike ya rubuta wani jawabi a ranar Laraba yana zargin INEC da buɗe wasu wuraren rajistar Katin Zaɓe a wasu Ƙasashe.


Download Mp3

Ya rubuta “akwai wuraren rajistar Katin Zaɓe a Jamhuriyar Nijar. To yaushe ne Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ta amince a gudanar da haka a wajen Najeriya.

“Miyasa Kafafen Yaɗa Labaru na Najeriya suka yi shiru akan haka. Shin suna goyon bayan wannan shirmen? Abun kunya ga aikin Jarida.”

Duk da shafin Nnabuike na karya ne, amma jawaban shi, sun tada ƙura.

Tuni wasu suka yaɗa abinda ya faɗa, ƴan kaɗan ne suka buƙaci bayanai daga INEC, Twitter, da Facebook tana suna kira da’a ƙaryata zargin.

A lokacin da aka zanta dashi a ranar Alhamis, Kwamishinan Hukumar, Shugaban Ɓangaren Ilmin masu kaɗa ƙuri’a, Festus Okoye, wanda yace bazai ce komai ba, amma ya bayyana jawabin a matsayin na ƙarya.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy