INEC ta bayyana Muhammad Abacha a matsayin dan takarar gwamnan Kano a PDP
Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta baiwa Muhammad Sani Abacha Fom din takarar gwamna a jam’iyar PDP a jihar Kano.
Hakan dai na nufin hukumar tayi watsi da dan takarar gwamna da jam’iyar ta fitar daga tsagin Aminu Wali wanda ke adawa da tsagin Shehu Wada Sagagi.
Jam’iyar PDP a Kano ta shiga rikicin shugabanci tun bayan ficewar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa jam’iyar NNPP.
Da yake tsokaci kan hakan, shugaban jam’iyyar PDP na Kano Shehu Wada Sagagi ya ce wannan abun yabawa ga hukumar INEC, sakamakon yadda ta duba cancanta wajen bayar da Nomination Fom din.
A karshe ya bayyana cewa wannan nasara itace zata basu kwarin gwiwa shiga zaben 2023, gadan gadan, domin nasara kan sauran jam’iyyu da zaka fafata kan kujerar gwamnan Kano.
