- Advertisement -

INEC Ta Koka Kan Karanci Masu Fitowa Don Mallakar Katin Zabe

0

INEC Ta Koka Kan Karanci Masu Fitowa Don Mallakar Katin Zabe - Dimokuradiyya

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana damuwa, kan samun karancin masu fitowa don mallakar katin zabe a jihar Katsina, duk kuwa da samar da Karin sabbin wuraren yin rijistar kusan 2000.

- Advertisement -

Kwamishinan zabe na hukumar a jihar Katsina Alhaji Jibril Zarewa ne ya shaida hakan yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na kasa.

Ya kara da cewa shekara guda kafin fara yin rijistar suka fuskanci za a samu karanmcin masu fitowa don karbar katin, hakan ya sanya suka shiga wayar musu da kai don amfanar su, amma duk da haka sai da aka samu da matsalar karancin su.

A cewarsa daga lokacin da suka dawo ci gaba da aikin a watan Maris, daga cikin cibiyoyin samar da katin 1,750, guda 1,200 basa iya samun mutane sama da 50 da suka je don mallakar katin zaben.

- Advertisement -

Ya kara da cewa hakan watakila ba zai rasa nasaba da yadda aka samu koma baya ba, biyo bayan katse layin sadarwa a jihar, wanda ya shafi kananan hukumomi 17 na jihar daga cikin 34.

Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Matsalar tsaro ce dai ta haddasa katse layukan sadarwa.

A karshe hukumar tayi kira ga mazauna yankunan da aka samar da cibiyoyin dama alummar jihar baki daya das u fita don mallakar katin zaben nasu, duba da muhimmancinsa gare su.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy