INEC Zata Aike Da Karin Na’urorin Yin Katin Zaɓe A Legas, Kano, da wasu Jihohi

0

INEC Zata Aike Da Karin Na’urorin Yin Katin Zaɓe A Legas, Kano, da wasu Jihohi - Dimokuradiyya

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC, tace zata tura ƙarin na’urorin yin rajistar zaɓe a wasu jihohin ƙasar nan saboda cunkoso da ake samu da kuma tarin cece kuce.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Juma’a tace laákari da cewa an fi samun cunkoson a jihohin Kano da Legas da kuma na yankin Kudu maso Gabashi, inda ta tura ƙari akalla na’urorin 209.

Kazalika hukumar kuma zata ci gaba da sa ido kan aikin na tsawon kwanaki sannan ta sake duba ci gaban da aka samu.


Download Mp3

Sai dai shugaban kungiyar al’ummar Fulani ta Miyetti Allah, ya nemi INEC din ta tsawaita jwa’adin aikin rajistar, inda yace akwai mambobin kungiyar da dama da ba su samu damar yin rijistar ba.

Kazalika kungiyoyin dake rajin kare hakkin dan Adam tuni suka maka hukumar a kotu, kan kin amincewa da sake Tsawaita wa’adin yin rijistar.

Sun dogara da cewa an Tsawaita lokacin zaben fidda gwanayen yan takara, don haka bai kamata ace yin rijistar an ki daga shi ba.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy