Jami’an Tsaron DSS Sun Ceto Mahaifiyar A.A Zaura Daga Hannun Masu Garkuwa A Jihar Jigawa

0

Jami’an Tsaron DSS Sun Ceto Mahaifiyar A.A Zaura Daga Hannun Masu Garkuwa A Jihar Jigawa - Dimokuradiyya

Sa’o’i 24 da sace mahaifiyar dan takarar sanatan kano ta tsakanin a jam’iyyar APC , A.A Zaura, jami’an tsaron DSS, sun kubutar da ita a wani wuri mai nisa a jihar Jigawa.

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki garin Zaura da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano tare da yin garkuwa da mahaifiyar Zaura a safiyar ranar Litinin.

An yi garkuwa da Hajiya Laure Mai Kunu da misalin karfe 4 na safe kafin fara kiran Sallar asuba.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace Hajiya Laure ne daga gidanta da ke kauyen Zaura mai tazarar kilomita biyar daga babban birnin Kano.


Download Mp3

Shugaban karamar hukumar Ungogo, Engr. Abdullahi Garba Ramat, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami’an tsaro ba su sanar da shi faruwar lamarin a hukumance ba.

Sai dai wani babban jami’in DSS da bai so a ambaci sunansa ba ya tabbatar da cewa mutanensu sun ceto Laure da wata tsohuwa da aka sace kusan kwanaki goma da suka gabata.

Ya ce, “Gaskiya ne mun ceto Laure a Jihar Jigawa, wannan ya biyo bayan wani kyakkawan bincike kan lamarin da mutanen mu suka yi. Mun gano ta a Jigawa, muka ceto ta ba tare da ta ji rauni ba”.

Hukumar ta DSS ta ci gaba da cewa yayin da suke kubutar da ita, sun gano wata tsohuwa wadda tuni aka biya kudin fansa Naira miliyan 2 daga cikin Naira miliyan 10 da suka nema, suka ceto ta.

A baya dai rahotanni sun nuna cewa masu garkuwa da mahaifiyar Zaura sun yi waya daga jihar Katsina, inda suka ce sun kai ta can.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargin suna da hannu a garkuwa da ita, wadanda ba a tantance ko su waye ba.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy