- Advertisement -

Jam’iyyar PDP Ta Yi Allah-Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Mambobinta A Jihar Kogi

0

Jam’iyyar PDP Ta Yi Allah-Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Mambobinta A Jihar Kogi - Dimokuradiyya

Daga: Abbas Yakubu Yaura

- Advertisement -

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kogi ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa mambobinta a karamar hukumar Ofu ta jihar Kogi.

PDP, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, mai dauke da sa hannun Daraktan Sadarwa Dayo Onibiyo, ta yi gargadi game da harin, inda ta ce “zai baiwa ‘yan sanda damar kammala bincikensu kafin daukar mataki.”

A baya Jaridar Dimokuradiyya ta rahoto cewa mutane da dama sun jikkata tare da lalata dukiyoyi bayan wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka mamaye wurin taron da matasan jam’iyyar PDP suke yi a Ologba dake karamar hukumar Dekina a jihar Kogi a ranar Litinin.

- Advertisement -

Jam’iyyar a cikin sanarwar ta ce ba za ta kasance kamar yadda ta saba ba yayin da jam’iyyar ke shirin tunkarar babban zaben 2023.

Onibiyo, ya yi kira ga mambobin kungiyar da su kwantar da hankalinsu duk da tsokanar da ake yi musu.

Ya kuma yi gargadin cewa jam’iyyar ba za ta sake nade hannunta ba, ta ga ana kai wa mambobinta hari ko kashe su.

- Advertisement -

A WANI LABARIN KUMA

Ƴan Sanda a Kano sun kama mutane biyu da ake zargin sun ƙware wajen satar wayoyin mutane da Makamai masu hatsari daga Matafiya, inda suke bayyana kan su a matsayin matuƙan a dai-dai ta ne.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar ga Manema Labaru a ranar Talata.

- Advertisement -

Yace Mohammed Jidda mai shekaru 20, da Adamu Suleiman Mai Shekaru 22, dukkanin su ƴan unguwar Birget, Kano, a halin yanzu suna nan a tsare a hedkwatar Rundunar dake Bompai, da karɓar wayoyin hannu da suke yi ga Mazauna Kano, a lokacin da suka hau Babur mai ƙafa uku.

Ya bayyana cewa sashen Rundunar Ƴan sanda na Puff Adder Suka kama su, bayan Kwamishinan Ƴan Sanda Sama’ila Dikko ya umarce su da su shiga su gudanar da aiki.

A cewar sa, wayoyi guda uku da suka sata an gano su

- Advertisement -

“An kama su ne bayan rahoto da aka samu cewa akwai wasu gungun Ɓarayi da suke nuna kansu a matsayin matuƙan adai-dai ta, suna karɓar wa mutane wayoyi akan hanyar Jahar, da Hanyar Tukur, da Hanyar Zaria da lamba KAROTA Number KBY 0126.

“Bayan samun wannan rahoton, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya Umarci Rundunar Puff Adder ƙarƙashin jagorancin Bashir Musa Gwadabe domin subi bayan su, su kama su.

Ya ce biyo bayan bincike, dukkanin su, sun amsa laifin su na cewa Ɓarayi ne, kuma sun ƙware wurin amfani da Babur mai ƙafa uku domin karbar wayoyin Al’umma.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy