- Advertisement -

Jaruman Izzar So sun kauracewa Taron Addu’ar Nura Mustapha Waye

0

Jaruman Izzar So sun kauracewa Taron Addu’ar Nura Mustapha Waye - Dimokuradiyya

A daidai lokacin da a ke cikin Jimamin rasuwar Daraktan fina finan Hausa, Nura Mustapha Waye, wanda Allah ya yi wa rasuwa a farkon wannan watan, Majalisar Dattawan Masana’antar Kannywwod sun Kira taron addu’a na Musamma.

- Advertisement -

PressHausa ta rawaito cewa an gudanar da taron ne domin addu’ar neman gafarar Allah ga Mamacin tare da sauran wadanda Allah ya yi wa Rasuwa tun daga kafuwar Masana’antar zuwa yanzu.

Taron wanda aka gudanar da yammacin jiya Laraba a Majalisar matasa ta Tarauni dake Unguwar Gyadi Gyadi a cikin garin Kano, an gudanar da Karatun Alkur’ani tare da addu’a ga Mamacin da Masana’antar Kannywwod.

Daga nan sai aka gabatar da nasihohi a game da hadin kai da yafewa juna domin samun tsira a wajen Allah.

- Advertisement -

Malam Khalid Musa, daya daga cikin Dattawan Masana’antar, ya ja hankalin ‘Yan fim da su guji Abubuwan da zasu jawo fushin Allah, a cikin Masana’antar domin samun tsira duniya da lahira.

Ya kara da cewa “Ita mutuwa ba jiran mu za ta yi ba, kowa mutuwar sa za ta zo masa ne ba tare da ya san ranar ba kamar yadda Nura Mustapha muka wayi gari da labarin mutuwar sa, to dan haka mu guji abin da zai kawo fushin Allah a Kan mu.”

Mutane da dama dai sun yi Jawabai da nasihohi sannan daga karshe aka rufe taron da addu’a.

- Advertisement -

Sai dai abin da mutane su ke ta yin magana a Kan sa dangane da taron addu’ar shi ne rashin Halartar da dama daga cikin Jaruman Izzar so wajen taron addu’ar, domin kusan in ban da Salisu S Fulani babu wani babban jarumin Izzar so da ya halarci taron.

Mutane sun yi mamakin rashin ganin Hajiya Nafisa, Aisha Najamu, Lawan Ahmad, (Umar Hashim) da Khadija Yobe da sauran manyan Jaruman.

PressHausa ta rawaito cewa, wasu na cewa ko dai yawon Galar Sallah suka tafi shi ya sa ba su je wajen ba, ko kuma.wani dalili mai kama da hakan, kasancewar yanzu ana tsaka da wasan sallah ne.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy