Jibia: NCS Ta Shawarci Al’ummomin Kan Iyaka Suyi Amfani Da Damar Yin Kasuwanci Don Bunkasa Tattalin Arziki

0

Jibia: NCS Ta Shawarci Al’ummomin Kan Iyaka Suyi Amfani Da Damar Yin Kasuwanci Don Bunkasa Tattalin Arziki - Dimokuradiyya

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta shawarci al’ummar Jibia da ke kan iyakar jihar Katsina da su yi amfani da damar kasuwanci a yankin, biyo bayan sake bude iyakokin da aka yi kwanan nan.

Ko-odinetan shiyyar NCS mai kula da shiyyar ‘B’ Kaduna, ACG Umar Garba, ne ya bayar da wannan shawarar a ranar Laraba yayin wata ziyarar sanin ya kamata a kan iyakar Najeriya da Nijar a karamar hukumar Jibia.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an bude kan iyakar Jibia ne a ranar 25 ga watan Afrilu bayan rufe ta a watan Agustan shekarar 2019.

Ya bayyana cewa sake bude kan iyakar ya sanya ’yan kasuwa da dama suka bunkasa a yankin, inda ya kara da cewa mazauna yankin da dama ne ke cin moriyar bude kan iyakar.

“Ina so in ba da shawara ga al’ummomin da ke kusa da wannan kan iyaka da su yi tunanin halaltattun kasuwancin tun lokacin da aka bude iyakar.

“Yin hakan zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin yankin, jihar da ma kasa baki daya.


Download Mp3

“Kamar yadda na fada masu, gwamnati ba ta son duk wani abu da bai dace ba kamar fasa-kwauri, fataucin yara, yaduwar kananan makamai.

“Idan duk wadannan abubuwan suna faruwa, da ba za a sami ci gaban tattalin arziki ba.

“Saboda haka, don Allah su yi amfani da sake bude kan iyakar a matsayin wata dama a gare su.”

ACG Garba ya kuma bayyana cewa ana shirin samar da na’urorin daukar hoto na zamani a kan hanya domin tabbatar da cewa ba a shigo da wasu haramtattun kayayyaki cikin kasar nan ba.

Ya kuma bayyana jin dadinsa da kyakykyawar alaka tsakanin al’ummomin kan iyaka da jami’an kwastam da sauran hukumomin tsaro da ma jami’an Jamhuriyar Nijar.

A nasa martanin sakataren karamar hukumar Jibia Alhaji Mohammed Lawal ya yabawa gwamnatin tarayya da hukumar NCS bisa sake bude iyakokin.

Ya kara da cewa tun bayan bude shi, kasuwancin da suka ruguje suna dawowa a hankali a cikin al’umma.

Lawal ya kuma yi kira ga hukumar NCS da ta taimaka wa al’ummar Jibia da ayyukan ‘yan bindiga suka raba da muhallansu a yankin.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy