- Advertisement -

Kada ku yanke ƙauna da ganin karshen matsalolin Najeriya – Gwamna Ganduje

0

Kada ku yanke ƙauna da ganin karshen matsalolin Najeriya – Gwamna Ganduje - Dimokuradiyya

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, ya yi kira ga al’ummar kasar nan da su kara zage damtse wajen yin addu’o’in neman kariyar Allah, tare da ganin karshen matsalolin tsaro da ake fuskanta.

- Advertisement -

A cikin sakon Barka da Sallah da kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa Najeriya na bukukuwan murnar zagayowar ranar idin babbar sallah.

Amma a gefe guda ana ci gaba da fuskantar barazana daga ‘yan fashi da ta’addanci duk da kokarin da gwamnati ke yi na shawo kan lamarin.

Sanarwar ta kara da cewa, “Muhimmancin bikin Sallah yana da matukar tasiri wajen samar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban Najeriya da kuma kokarin da kasar ke yi na shawo kan matsalolin tsaro.”

- Advertisement -

Ganduje ya kuma jaddada bukatar zurfafa tunani a kan darussan bikin da suka hada da sadaukarwa, soyayya, zaman lafiya da juna.

Ya lura da cewa al’ummar kasar na shirin gudanar da zafafan harkokin siyasa, akwai bukatar magoya bayan yan siyasar, su rika kiyayewa da ka’idojin siyasar.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani abu da ka iya jawo asarar rayuka da dukiya ba.

- Advertisement -

Gwamnatinsa ta zage damtse wajen samar da zaman lafiya wanda ya bayyana a matsayin mai kawo cigaba ga kowace al’umma, sannan ya kuma yi kira ga al’umma da su fahimci ma’anar wannan biki da kuma koyi da darussa na biyayya da sadaukarwa kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna.

Yayin da yake taya al’ummar musulmi barka da sallah, gwamnan ya yi fatan gudanar da bukukuwan sallah lafiya.

- Advertisement -
wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy