Kamfanin Rarraba Hasken Lantarki Na Kano, Jigawa, Katsina Ya Ɓara

0

Kamfanin Rarraba Hasken Lantarki Na Kano, Jigawa, Katsina Ya Ɓara - Dimokuradiyya

Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki a jihohin Kano, Jigawa, Katsina KEDCO ya bayyana dalilan da suka janyo karancin samun wutar a Jihohin.

A cewar kamfanin wutar bata samuwa daga hukumar samar da wutar lantarkin ta ƙasa, hakan shine ya sanya suna basu da wadatacciyar Wutar da zasu baiwa abokan hulɗar su kamar yadda suka saba a baya.

KEDCO ya ce bisa rahotannin da suka samu ana samun Megawett 1,357MW wanda ake bawa KEDCO Megawett 150MW kacal daga wancan adadi.


Download Mp3

A sanarwar da kamfanin ya fitar ta hannun mai magana da yawun kamfanin Ibrahim Sani Shawai ya ce Megawatt 150MW din da suke samu ita ce suke rabawa ga jihohi ukun da suke ƙarƙashin su.

Ibrahim Shawai ya ƙara da cewa suna raba wutar ce ta hanyar yin adalci ba tare da wata jiha tafi wata samun wutar ba.

A ƙarshe ya tabbatar wa da abokan hulɗar su cewa nan ba da jimawa ba za a a samu wadatar wutar kamar yadda aka saba.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy