Kano: An Samu Ƙaruwar laifin Cin Zarafin Mata A Watan Mayu – CITAD

0

Kano: An Samu Ƙaruwar laifin Cin Zarafin Mata A Watan Mayu – CITAD - Dimokuradiyya

Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban Al’umma CITAD, ta bayyana damuwa kan yadda ake samun karuwar cin zarafin mata a jihar Kano.

Kungiyar ta ce ci gaba da tashe-tashen hankula da ake fama da su a kan jinsi abin bakin ciki ne don haka, akwai bukatar dukkan bangarori su tashi tsaye tare da hada hannaye domin yakar matsalar.

Jami’ar fasaha ta Cibiyar, Zainab Aminu, ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da manema labarai a kan rahoton cin zarafin mata da aka samu ta hanyar wayar salula ta cibiyar a watan Mayu 2022.

Zainab ta bayyana cewa “Idan aka kwatanta da bayanan da aka samu a watannin baya, har yanzu matsalar cin zarafin mata tana karuwa”.

Ta lura cewa, “An ba da rahoton kararraki 85 ta hanyar GBV App na cibiyar a watan Mayu wanda ya hada da Fyade,”

Ta bayyana cewa bayanan da aka tattara a watan Mayu na nuni da yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a jihar Kano wanda ke bukatar tsayuwar daka wajen shawo kan wannan annoba.

“Muna kira ga jama’a da su rika kai rahoton cin zarafi da suka shafi jinsi ga hukumomin da abin ya shafa.

Kuma muna kira ga gwamnati da ta kara kaimi wajen sanya dokokin da za su kare mata daga matsalar cin zarafin su, ta yadda masu aikata ta’addanci su kau da kai daga irin wadannan ayyuka”.

A karshe Zainab ta yi kira ga mahukuntan makarantu da su samar da wata tawaga ta masu sa ido da za su sanya ido tare da bayar da rahoton cin zarafi a cibiyoyinsu tare da yin kira ga malamai da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na kula da dalibai.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy