Kano: Kudirin Karin Shekarun Ritaya Ga Malaman Firamare da Sikandire ya tsallake karatu na 2

0

Kano: Kudirin Karin Shekarun Ritaya Ga Malaman Firamare da Sikandire ya tsallake karatu na 2 - Dimokuradiyya

Majalisar dokokin Kano tayi karatu na biyu kan kudirin dokar karawa malaman makarantun firamare da sakandire wa’adin shekarun ajiye.

Kudirin dai na magana kan yadda za a kara wa’adin aiki ga malaman daga shakara 35 zuwa 40 da kuma shekarun ajiye aiki na haihuwa daga 60 zuwa 65.

Majalisar karkashin shugabanta Hamisu Ibrahim Chidari, ta amince da karatu na biyu kan kudirin ne a zamanta na Talatar nan.

Majalisar ta kuma baiwa kwamitin ilimi na majalisar da yayi nazari akan kudirin tare da gabatar da rahotansa nan da kwana arba’in.

Idan za a iya tunawa a ranar Laraba 15 ga watan da muke ciki ne majalisar dokokin tayiwa kudurin karawa malaman makarantar wa’adin shekarun ajiye aiki karatu na farko.

Haka zalika majalisar ta amince da karatu na biyu kan kudirin dokar daga darajar asibitin Abdullahi Wase da akafi sani da asibitin Nasarawa zuwa asibitin koyarwa.

ADVERTISEMENT

Daga darajar asibitin zuwa asibitin koyarwa zai baiwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule, da Jami’ar Kimiya da Fasaha ta Aliko Dangote, dake Wudil, damar bude tsangaya da sashin koyar da ilimin likitanci.

Majalisar ta baiwa kwamitin lafiya da kwamitin ilimin manyan makarantu na majalisar yin nazari tare da gabatar da rahotansu bayan dawowa daga hutun sallah.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy