Labaran Wassanin A Wannan Lokaci Yanayi Ya Nunah Cewa Wata Kilah Salh Zaije Barcelona. 

Kocin Barcelona Ronald Koeman yana son mayar da hankali wurin dauko dan wasan Liverpool da Masar Mohamed Salah, mai shekara 28, a cewar jaridar Sunday Express

Jaridar ta kara da cewa Manchester United za ta iya yunkurin dauko dan wasan Real Madrid da Wales Gareth Bale, mai shekara 31, a matsayin zabin da ya rage mata kan dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20. (Sunday Express)

Dan wasan Sufaniya Sergio Reguilon, mai shekara 23, ya fi son tafiya zaman aro a Sevilla maimakon komawa Manchester United. (AS – in Spanish)

An ki amsa tayin Tottenham na karbo aron dan wasan Torino da Italiya mai shekara 26 Andrea Belotti. (Sky Italia – in Italian)

Manchester United ta shirya biyan £23m don dauko dan wasan Monaco dan kasar Faransa Benoit Badiashile, mai shekara 19. (L’Equipe, via Sunday Express)

Kocin Inter Milan Antonio Conte yana son dauko dan wasan Chelsea da Sufaniya Marcos Alonso, mai shekara 29. (Sky Italia, via Mail on Sunday)

Tottenham na duba yiwuwar dauko dan wasan pondering Braga dan kasar Portugal Paulinho, 27. (90min)

Dan wasan Manchester City da Ukraine Oleksandr Zinchenko, mai shekara 23, zai kasance cikin musayar da kungiyar za ta yi don dauko dan wasan Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29. (Radio Marte, via Sun)

Tsohon dan wasan Manchester City da Ivory Coast Yaya Toure, mai shekara 37, ba shi da niyyar yin ritaya kuma yana son murza leda a Serie A. A halin yanzu ba shi da kungiya bayan barin kungiyar Qingdao Huanghai a kasar China a watan Janairu. (Tuttomercato via Goal)

West Ham na sha’awar dauko dan wasan Brighton mai shekara 26 Solly March kuma ta soma tattaunawa a kan hakan. (90min)

An ki amsa tayin euri 17m da Aston Villa ta bayar don dauko dan wasan Lyon da Burkina Faso Bertrand Traore, mai shekara 25.(Footmercato – in French)

Ku Tura Zuwa Facebook WhatsApp Twitter Instagram Da Sauran Social Media.

Zaku Iya Samun Sabbin Labaran Kannywood Da Sabbin Wakokin Siyasa Dana Hausa Duk Wannan Shafin.