Kotu Ta Yanke Wa ‘Mama Boko Haram’ Da Wasu Mutane 2 Hukuncin Zaman Gidan Yari Kan Zambar Naira Miliyan 71.4

0

Kotu Ta Yanke Wa ‘Mama Boko Haram’ Da Wasu Mutane 2 Hukuncin Zaman Gidan Yari Kan Zambar Naira Miliyan 71.4 - Dimokuradiyya

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, shiyyar Maiduguri, ta samu nasara kan yankewa Aisha Alkali Wakil, wacce aka fi sani da “Mama Boko Haram”, tare da wani mai suna Yarima Lawal Shoyode da Tahiru Sa’idu Daura hukuncin wanda mai shari’a Aisha Kumaliya ta babbar kotun jihar Borno dake Maiduguri tayi.

Kakakin Hukumar, Wilson Uwujaren, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Talata.

Ya ce an yanke wa wadanda ake tuhumar hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyar a ranar Talata ba tare da zabin biyan tara ba.

“Hukuncin shine babban matakin da ya fara a ranar Litinin, 14 ga Satumbar shekarar 2020 lokacin da aka sake gurfanar da wadanda ake tuhuma a kan tuhume-tuhume biyu na hada baki da kuma karbar kudi ta hanyar karya daya kai Naira Miliyan Saba’in Da Dari Hudu 71,400,000, kawai”, ya kara da cewa.

A wani labarin kuma, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Sakkwato ta biya kudin gidaje akalla 70 da aka tantance wanda guguwar iska ta lalata a unguwar Al-Hassan da ke karamar Hukumar Tambuwal a Jihar Sakkwato.

Da yake jawabi yayin karbar bakuncin jami’an SEMA karkashin jagorancin babban daraktan hukumar, Nasir Aliyu, hakimin gundumar Tukur Tambuwal, ya bayyana cewa gidaje kusan dari ne guguwar ta shafa.

Ya yabawa Gwamna Aminu Tambuwal bisa yadda ya amsa kukan al’umma.


Download Mp3

A yayin da ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta taimaka wa wadanda suka yi asarar kadarorinsu da guguwar talalata, ya ce galibin gidajen da abin ya shafa sun lalace ba tare da gyara ba.

A nasa jawabin, babban daraktan hukumar SEMA na Sokoto, Nasir Aliyu, ya tabbatarwa da hakimai da kuma wadanda abin ya shafa cewa hukumar za ta yi duk mai yiwuwa don tallafa musu.

Ya ce, “Mun zo nan ne domin a tantance irin barnar da aka yi kuma mun zagaya don ganin al’amura da kanmu ma.

“Mun kuma ga jerin sunayen wadanda abin ya shafa wanda hakan wata babbar alama ce da ke nuna cewa ku da wadanda ke karkashin ku kuna aiki cikin jituwa.

“Wasu wuraren kuma, za a dauki kwanaki bayan ziyarar tantancewar kafin mu samu jerin sunayen.

“Muna tabbatar muku da cewa za mu yi aiki a cikin jerin da aka tanadar mana a nan ba tare da damuwa ba idan muka ziyarci tsarin ku ko a’a.”

Shima da yake nasa jawabin shugaban karamar hukumar hTambuwal Honorabul Nasir Tambuwal ya yabawa gwamnatin jihar bisa wannan ziyarar.

Ya bukaci SEMA da ta rubanya kokarinta na kawo agaji ga wadanda abin ya shafa domin rage musu radadin barnar.

Ya ce yawancin wadanda abin ya shafa sun zama marasa gidaje, suna kwana da abokai da ‘yan uwa ko kuma a sakatariyar karamar hukumar.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy