- Advertisement -

Kotun Jahar Kebbi Ta Yankewa Wani Mutun Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Har Sai Ya Mutu – Bayan Ya Aikata Mummunan Kisan Rayuwa Biyu

0

Kotu ta yanke hukuncin kisa ga Sulaiman Idris da ya kashe matar aure da diyarta a Unguwar Labana Birnin Kebbi.

Wata babban Kotun jihar Kebbi da ke zamanta a garin Birnin kebbi ranar Laraba 6 ga watan Yuli ta yanke wa Suleiman Idris hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta kama shi da laifin kashe Sadiya Idris da diyarta.

- Advertisement -

Mai shari’a Jastis Muhammad Sulaiman Amburrsa ya kama Sulaiman da laifin kisa ne bayan ya ki amincewa da uzurin da Lauyan Sulaiman ya kawo cewa mariganya Sadiya ta harzuka Sulaiman ne watau “Provocation”.

Lauyan ya ce Sadiya ta gaya wa Sulaiman kalamai da suka bata masa rai, cewa “Jahili wulakantaccen maigadi…” da dai sauransu.

Sai dai Kotu ka ki amincewa da uzurin bisa hujjar cewa Sadiya ta gaya masa kalaman ne da misalin karfe 10 na safe, amma sai karfe 2 na dare ya je ya kashe ta. Kotu ta ce abin da Sulaiman ya aikata ya zarce abin da Sadiya ta yi masa, kari da cewa diyarta bata yi masa laifi ba amma duk ya kashe su.

- Advertisement -

Sakamakon haka Alkalin Kotun Muhammad Sulaiman Ambursa ya kama Sulaiman Idris da laifin kisan Sadiya da diyarta kuma Kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya har sai ya mutu.

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy