Wani Hanzari Ga Gudu Bah, Ga Iyaye Maza Da Mata Yadda Ya Kamata Su Karantawa ‘Ya ‘Yan Hakkin Zaman Aure.

Hakkin iyaye ne su aurar da ‘ya’yansu mata da maza a lokacin da su ka kai munzalin aure, kuma hakki ne a kansu su fayyace mu su yadda a ke yin zaman auren da abin da ya ke cikin auren da yadda a ke yin zaman auren. Tabbasa samari da ‘yan mata sun a zaton aure abu ne na nishadi da holewa da kuma nuna bajinta ba tare da sun san menene auren ba da yadda zaman auren yak e ba.

Dan haka daga an gama hidimar biki an cika gida da kayan alatu sai su yi zaton soyayya kawai za a yi ta yi babu sauran kalubale, ba haka abin ya ke ba kuma a zahiri. Yau da gobe sai Allah, kuma zo mu zauna an ce zo mu saba in ji ma su iya magana.

Aikin uwa mace ne ta zaunar da ‘yar ta ta karanto ma ta duk wani hakkin mijinta da ya ke kanta da kuma yadda za ta zauna da shi da kuma danginsa . Ladabi da biyayya ne akan gaba sai kuma tsafta da iya abinci kuma a dafa akan lokaci ba sai miji ya dawo da yunwa ba sannan za a hau fafutukar dora tukunya.

Haka uba namiji ya zaunar da dansa ya fada ma sa yadda ya kamata ya kula da matarsa, ya sauke hakkin da Allah ya dora ma sa na ciyarwa da tufatarwa da kuma muhalli.

Gaba daya mace da namiji su na da bukatar a fada mu su a sake fada mu su wannan kalma ta ‘hakuri” tabbas zaman aure ba zai taba a yiwuwa ba idan babu hakuri.

Mace-macen aure ya yi yawa a a rewacin Najeriya a sanadiyyar rashin hakuri abu kalilan sai ya jawo saki.

Zawarawa sun yi yawan da har ba a shakka kuma ba a jin nauytin ambaton saki sabo da ya zama ruwan dare.

Abin mamaki kuma sai a samu hannu uwar miji ko uwar mata dumu-dumu wajen ba da gudunmawa aure ya mutu.

Iyaye da yawa su na taka rawa wajen hargitsa zaman auren ‘ya’yansu saboda son abin duniya ko wata manufa ta daban akan burinsu.

Wata uwar ita ta ke kimtsawa ‘yar ta yadda za ta bi da miji ta hanyar gurbatatcciyar hanya dan a kori kishiya ko a hana shi kara aure ko kuma a mallake shi ya guji danginsa da mahaifansa duk abin da ya samu ita kadai da iyayenta zai din ga yiwa.

Ba kullum ake kwana a gado ba kuma idan yau sun yi nasara gobe dubunsu za ta iya cika miji ya farga, ko ya kama ta da hannu dumu-dumu ta na zalumtarsa a take zai ya sake ta. Irin haka wa gari ya waya?

Dan haka iyaye musamman mata ya kamata su dukufa wajen bawa yaransu shawara ta gari yadda za su zauna da kowa lafiya a gidan aure idan sun yi kuskure a gyara mu su. Idan kawayen banza ne su ke zuga ta, ayi marmaza a raba ta da su don za su kai ta su baro ta.

Haka uwar miji mai takurawa suruka har sai ta ga ta kashe auren sannan hankalinta zai kwanta wannan ba tarbiyya ba ce, amma kuma ita ta na so yaranta mata da ta aurar su yi zaman aure lafiya a wani gidan.

Duk sai mun taru mun raya sunnar aure idan ba haka ba duk auren da aka yi kafin a gama biyan kudin ankon auren ya mutu dan haka zawarawa sun cika gari har sun fi ‘yan matan da ba su taba yin auren ba ma yawa.

Ina Mafita?

1. Ya kamata iyaye su dinga fadakar da matasa kafin a aurar da su akan yadda aure yake.

2. Ya kamata iyaye su ding aba da musali akan yadda su kansu su ke zaman lafiya a gaban yaransu yadda za su koya da kansu ko ba a fada mu sub a.

3. Cikin lallashi da zare ido a fadawa ‘yan mata ma su shirin yin aure akan dole ne su yiwa mazan su biyayya bayan an yi aure.

4. A gargadi namiji da saurin yanke hukuncin saki ba tare da ya tuntubi many aba ko me matar ta yi ma sa.

5. A gargadi matasa da yin abokai barkatai ma sub a su muguwar shawara akan zaman aure.

6. Mace da namiji su cire mugun kishi da zargin juna a cikin zaman aurtensu.

7. Kowannensu sai ya karanci yadda halin dayan yake dan a kiyaye abinda bay a so a zauna lafiya.

8. A gargadi matasa ka da su gina soyayya akan karya da kwadayi. A yi kauna ta tsakani da Allah bad an abin duniya ba.

10. Iyaye su gargadi yaransu ma su shirin yin aure da su guji sharrin zuciya, a dinga kai zuciya nesa ka da cacar baki da musu ya hada su wani ya jawo makami ya hallaka dayan.

Kada Ku Manata Zaku Iya Samun Sabbin Labaran Kannywood Da Sabbin Wakokin Siyasa Dana Hausa Duke A Cikin Wannan Shafin Namu Dake Kokarin Faranta Muku Rayukan Ku.

Zaku Iya Turawa Zuwa Facebook WhatsApp Twitter Instagram Da Sauran Social Media Domin ‘Yan Uwan Ku Su Karu Da Wannan Post.

Kada Kuyi Kasa A Guiwa Ku Ajiye Munah Comments Dinku Domin Jin Ra’ayoyin Ku Da Bukatun Ku.

Zaku Iya Turo Munah Sako Ta Wannan Email Kamar Haka:- info@pressloadedng.com Ko PressLoaded2@Gmail.com Mungode.