Ku Samar Da Sabbin Dabaru Dan Magance Matsalar Rashin Aikinyi A Tsakanin Matasa – Hassan Gusau

0

Ku Samar Da Sabbin Dabaru Dan Magance Matsalar Rashin Aikinyi A Tsakanin Matasa – Hassan Gusau - Dimokuradiyya

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Hassan Mohammed Gusau, ya yi kira ga shugabannin gargajiya da su kara kaimi wajen tallafa wa matasa a fannin ilimi da sanin makamar aiki don dogaro da kai.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labaran gwamnan jihar, Babangida Umar Zurmi ya sanyawa hannu tare da raba wa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar.

Sanarwar ta ce, Gusau ya yi wannan kiran ne a lokacin da sarkin Gumel Ahmad Mohammed Sani ya nada Nasiru Mohammed Waziri a matsayin sarkin Bunun Gumel ta Jihar Jigawa.

Mataimakin Gwamnan ya ce ba shi da tantama cewa sabon Rawani Bunin Gumel zai daukaka darajar marasa galihu da kuma matasa.

Na san shi mai taimakon jama’a ne, kuma ba ni da shakka a raina cewa zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na alheri musamman a yanzu da ya zama shugaban gargajiya.” Ya kara da cewa.

Mataimakin Gwamnan ya yi kira ga Bunun Gumel da ya kara habaka hanyoyin da zai dore da ayyukan sa na alheri tare da tabbatar da ci gaba da bullo da sabbin dabaru na daukar karin matasa a fannin ilimi da ci gaban bil Adama a Masarautar.

Mataimakin Gwamnan ya samu rakiyar Sanata Adedebu, Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Kwalejin Kimiyya ta Jihar Zamfara Gusau Alhaji Abubakar Lawali Gusau, Darakta Janar na na tsare-tsare Abdullahi Lawal Maradun Babangida, Babban Sakatarensa mai zaman kansa, Dakta Ahmad Lawal da dai sauransu.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy