Kuje Kotu idan baku yarda da Sakamakon Zaben Fidda Gwani — PDP ga ƴan Takara a Ogun

0

Kuje Kotu idan baku yarda da Sakamakon Zaben Fidda Gwani — PDP ga ƴan Takara a Ogun - Dimokuradiyya

Kuje Kotu idan baku yarda da Sakamakon Zaben Fidda Gwani — PDP ga ƴan Takara a Ogun

Jam’iyyar PDP a Jahar Ogun tayi kira ga Fusatattun Ƴan Takarar Gwamna guda biyu dasu je Kotu tare da neman haƙƙin su, idan basu gamsu da sakamakon Zaben Fidda Gwani da aka gabatar a ƴan kwanakin nan.

Dayake jawabi ga Manema labaru a Sakatariyar Jam’iyar dake Abeokuta, Babban Birnin Jahar Ogun, Shugaban Jam’iyyar Sikirulahi Ogundele yayi kira ga ƴan Takara Segun Showunmi da Jimi dasu sanya Jam’iyyar a cikin zuciyar su.

Ogundele ya ayyana Fusatattun Ƴan Takarar dake cewa sun samu nasara a matsayin masu neman tada zaune tsaye.


Download Mp3

Yace Dan Takarar da aka zaba a PDP a Jahar Ogun shine Oladipupo Adebutu, kuma babu wani sai shi.

Showunmi a ranar 25 aka gudanar da zaɓen fidda Gwani inda aka zaɓe shi a matsayin Ɗan Takarar Gwamna.

Lawal, wanda ya jagoranci Zaben Fidda Gwani daya fitar da Adebutu a matsayin Ɗan Takarar, yayi kira da aka soke zaben a Jahar, yana mai cewa sunayen Deliget da aka yi amfani dasu wajen zaɓen bana gaskiya bane.

Amma Jam’iyyar PDP tace bata yi wani zaɓen fidda Gwani guda a ko’ina.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy