Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu Ta Ƙaryata Zancen da ake Yaɗawa Kan Dan Takarar

0

Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu Ta Ƙaryata Zancen da ake Yaɗawa Kan Dan Takarar - Dimokuradiyya

Kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa, ta Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ta bayyana cewa wasu kafafen yada labarai sun fassara kalaman da dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu yayi ba daidai ba.

Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Tinubu, a wata ziyarar tuntuba da ya kai wa wakilan jam’iyyar APC a jihar Ogun, ya bayyana yadda ya sanya shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi nasara a zaben shugaban kasa a 2015.

Baya ga shugaban kasa Muhammad Buhari kazalika Tinubun ya taimakawa gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, shima ya dare zuwa mukamun Gwamna.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan yakin neman zabe da hulda da kafafen yada labarai, Bayo Onanuga, a yau Juma’a, ta bayyana kalaman Tinubu a matsayin kuskure da aka aikata gare shi domin kuwa ba haka yake nufi ba.

Onanuga ya bayyana cewa kalaman Tinubu sun kasance a cikin jama’a kuma sun kasance gaskiyar da aka yi nazari shekaru da yawa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “An jawo hankalin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan kuskure, yaudara da kuma mummunar fassarar da aka yiwa jawabin Tinubun a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun ranar Alhamis.

“A bisa bayanan cewa jigo a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga wakilan jam’iyyar na kasa a jihar Ogun, tare da gwamna Dapo Abiodun.

“Kungiyar yakin neman zaben ta na yin kira ga kafafen yada labarai da su guji tada hankalin jama’a na gaskiya tare da taka rawar da kundin tsarin mulki ya tanada na sanar da masu zabe da su yi zabi na gaskiya a zaben fidda gwani na shugaban kasa,” in ji sanarwar.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy